Connect with us

Uncategorized

Cutar Lassa Fever ya dauke rayuka 5 a Jihar Plateau

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mumunar cutar da ake ce da ita ‘Lassa Fever’ ya dauke rayukan mutane biyar a Jihar Jos a ranar Lahadi 28 ga Watan Janairu da ta gabata.

Kwamishanan Kulawa da Lafiyar jiki na Jihar, Dokta Kunden Deyin ya bayyana wa Hukumar Labarai na Kasar Najeriya (NAN) a ranar Lahadi da ta wuce da cewa sun sami rahoton alamun wannan cutar a wurare goma sha bakwai 17 a nan Jihar, bayan mutane 5 da suka mutu.

Doktan ya bayyana da cewa kimanin mutane goma sha ukku 13 ke asibitin don kulawa a halin yanzu, wasu kuma an rigaya an sallame su daga kulawar. “Akwai kimanin mutane 73 da aka kuma gano da alamun cutar, a halin yanzu ana bincike na tsawon kwanaki 21 don tabbatar da alamun da kuma daukar mataki a gaggauce don magance cutar” in ji shi.

“Idan har bayan binciken kwanaki 21 muka gane da cewa akwai wadanda basu kamu da cutar ba, zamu sallame su, idan kuwa an sami wasu daga cikin su da cutar sai a nuna masu kulawa da ta dace” in ji shi.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Cutar ‘Lassa Fever’ ya kashe wani Sojan Najeriya da ke a barikin Rukuba ta Jihar Jos.

Ya kuma shawarci duk wasu masu jin ciwon kai, ciwon jiki ko kuma wata alamun ciwo da basu gane da shi ba, da cewa su je a masu bincike isasshe don tabbatar da cewa ba cutar bane suka kamu da shi”.

Ko da shike mun sanar a Naija News Hausa a kwanakin baya da cewa Shugaban Hukumar (NCDC), mai suna Dokta Chikwe Ihekweazu ya fada da cewa kada ‘yan Najeriya su tsorata da kamuwar cutar ‘Lassa Fever’, don sun rigaya sun samar da matakai don magance yaduwar cutar a kasa.

Dokta Deyin ya bayyana da cewa abin kaito ne da cewa wasu basa zuwa bincike lokacin da suka gane da wata ciwo a jikunan su sai har abin ya cije da gaske kamin su je asibiti don kulawa.