Labarai Hausa
Ku sadaukar da makaman ku, IGP na gayawa masu amfani da bindiga da ba kan doka ba

IGP Mohammed Adamu, Sabon shugaban Jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari ya sanya kwanakin da suka shiga bayan da aka dakatar da Ibrahim Idris, tsohon shugaban jami’an tsaron ya umurci duk wadanda ke da bindigogi da makamai a gidan su da doka bata bayar ba cewa su sadaukar da makaman ga jami’an tsaro kamin ya dauki mataki akan haka.
Naija News Hausa ta ruwaito da cewa IGP Adamu ya gabatar’ yan lokatai da suka wuce a ranar yau da cewa “An dakatar da bada dokar Izinin amfanin da bindiga ko wata makami a kasar Najeriya“.
IGP Mohammed Adamu ya gabatar da hakan ne daga bakin kakakin hukumar Jami’an tsaron kasar Najeriya, ACP Frank Mba a ranar Lahadi 27, ga Watan Janairu, 2019 a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
IGP ya sake gabatar da wannan ta shafin nishadin twitter din shi dan tabbatar da muhimancin wannan ga ‘yan Najeriya duka da ke ajiye da makamai a gidajensu da cewa “Ku sadaukar da makaman ku, Akwai hukumci da zai biyo baya ga duk wadanda basu kiyaye wannan umurni ba” in ji Mohammed Adamu.
Ga Sanarwan kamar haka a shafin twitter na IGP;
PROLIFERATION OF ILLICIT WEAPONS:
– IGP Calls for Voluntary Surrender of Weapons
– Places Embargo on the issuance of New Arm Licences
– Warns of Dire Consequences for Defaulters pic.twitter.com/G0SlIj3pSw— Nigeria Police Force (@PoliceNG) January 28, 2019
Naija News Hausa ta ruwaito da cewa IGP Adamu ya gabatar Makon da ta gabata da cewa, “Ba tsaro kawai zamu samar da shi ba, harma da kare damar al’ummar Najeriya duka” inji IGP Mohammed.
