Connect with us

Uncategorized

Mahara da Bindiga sun kai sabuwar hari a wata Gidan Kallon wasa a Jihar Zamfara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mun sami rahoto a Naija News Hausa da cewa wasu ‘Yan Hari da Bindiga da ba a san da su ba sun kai sabuwar hari a Jihar Zamfara a wata Gidan Kallon Wasan Kwallon kafa da ke nan yankin Birnin Magaji, a Jihar.
Kimanin mutane bakwai ne aka sace a lokacin da ‘yan hari da bindigan suka fada wa gidan kallon wasar a ranar Asabar da ta gabata a nan yankin Birnin Magaji.

Mallam Sanusi Iliyasu Ishie, wanda ke da Gidan kallon ya ce “Sun bar motar su ne da nisa kadan da gidan kallon kamin suka haro wajen da tambayar wanda ke gudanar da kallon”.

“Sun kai kimanin mutane 20 da suka hari gidan kallon, Isowar su a wajen kallon misalin karfe 10:00 na dare, sai suka tambayi mai jagoran Gidan kallon, ni kuma da jama’ar da ke wajen muka amsa masu da tunanin cewa jami’an tsaro ne ba tare da sanin cewa ‘yan hari da bindiga ne ba” in ji Mallam Sanusi.

“Da jama’ar da ke gidan kallon suka gane da cewa ‘yan hari da bindiga ne, sai kowa ya ita kokarin gudun hijira, da kuwar taimako ga jama’a”.
“Da ‘yan harin suka ga haka, sai suka kame mutane shidda daga cikin taron” inji shi.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun yi barazanar kashe ‘yan ta’adda 58, ribato 78 a tsakanin Kaduna, Katsina da Zamfara ‘yan kwanakin da suka wuce.

Ofisan Yada Labarai da Cudanya na Jami’an tsaron ‘yan Sanda da ke a Jihar, Muhammad Shehu ya bayyana da cewa Jam’iyyar tsaron bata samu cikakken bayani ba a lokacin da aka bincike su da bayyani akan abin da ya faru.

Ko da shike muna da sani a Naija News Hausa da cewa Jihar na cikin muggan hari a koyaushe tun ‘yan lokatai da daman da nan.

 

Karanta wannan Kuma: Kimanin mutane Ukku suka rasa rayukan su a Jihar Nasarawa sakamakon wata hari da Mahara da bindiga suka kai wa Jihar.