Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini 28, ga Watan Janairu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini 28 ga Watan Janairu, 2019

 

1. Gwamnatin Buhari ta mayar da Martani ga US, UK, EU akan CJN Onnoghen

Gwamnatin kasar Najeriya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta kalubalanci kasar US, da wasu kasashen Turai da cewa su kauche bakin su game da al’amurar kasar Najeriya.

Kamar yadda muka sanar a Naija News da baya da cewa Shugaba Buhari ya dakatar da babban Alkali kasar Najeriya, Alkali Onnoghen a ranar Jumma’a da ta gabata kuma ya sanya Tanko Mohammed a matsayin sabon babban alkalin kasar Najeriya.

2. IGP Adamu ya dakatar da izinin amfani da makamai ga jama’a

Sabon shugaban Jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ya dakatar da dokar izini na amfani da makamai ga al’umma a kasar Najeriya.

An sanar da wannan umurnin ne daga bakin kakakin hukumar, ACP Frank Mba a ranar Lahadi 27, ga Watan Janairu, 2019 a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

3. ‘Yan Ta’addan Boko Haram sun kai farmaki ga rukunin Sojojin Najeriya

‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai sabon hari a rukunin sojojin Najeriya da ke a Jihar Borno daren Lahadi da ta gabata har sun yi wa mutane shidda raunuka sakamakon harbe-harben da suka yi, kamar yadda aka samu tabbacin hakan ya faru daga bakin jami’an tsaron biyu.

Wannan shine babbar hari da ya auku a Jihar tun da dadewa, kamar yadda tsaro ya zama da matsala a jihar da kuma gudanar da yakin neman zabe.

4. Abin da Femi Falana ya gabatar game da dakatar da Onnoghen

Lauyan Hakin Al’umma, Femi Falana ya ce “abin mamaki ne ganin irin yadda Alkalai da shugabannan shari’a suka fada ga hakon makiya don tabbatar da dakatar da babban Alkalin kasar, Alkali Walter Onnoghen” a matsayin babban shugaban Alkalan kasar Najeriya.

Mun sanar a Naija News a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da babban Alkalin kasar Najeriya, Walter Onnoghen a ranar Jumma’a da ta gabata, ya kuma sanya Tanko Mohammed a matsayin sabon shugaba alkalan kasar.

5. Hukumar INEC ta wallafa sunayen mutane 144 da zasu yi kular gefe da zaben 2019

Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC), ta saki sunayan mutane 144 a ranar Lahadi da ta gabata da zasu gudanar da kulan gefe ga zaben tarayya ta shekarar 2019 da ke gaba.

Naija News ta sanar a baya da cewa hukumar ta gabatar da cewa zasu dakatar da duk wata jam’iyya da mamban ta ta aikata halin da bai dace ba.

6. Femi Falana yayi kira ga shugaba Buhari da daga zancen dakatar da Alkali Onnoghen

Lauyan Hakin Al’umma, Femi Falana (SAN) yayi kira ga alkali Walter Onnoghen da cewa ya manta da batun hukumar ganin irin yawan zargi da suke akan shi.

Lauyan, Mista Falana yayi kira kuma ga shugabancin Muhammadu Buhari da ta manta da zancen dakatar da babban alkali Onnoghen.

7. Cutar Lassa Fever ya dauke rayuka 5 a Jihar Plateau

Mumunar cutar da ake ce da ita ‘Lassa Fever’ ya dauke rayukan mutane biyar a Jihar Jos a ranar Lahadi 28 ga Watan Janairu da ta gabata.

Kwamishanan Kulawa da Lafiyar jiki na Jihar, Dokta Kunden Deyin ya bayyana wa Hukumar Labarai na Kasar Najeriya (NAN) a ranar Lahadi da ta wuce da cewa sun sami rahoton alamun wannan cutar a wurare goma sha bakwai 17 a nan Jihar, bayan mutane 5 da suka mutu.

8. IGP Mohammed Adamu ya dakatar da dukan DIGs da ke karkashin sa

Sabon shugaban Jami’an tsaron ‘yan sanda Najeriya da aka sanya kwanaki kadan da suka wuce,  Muhammed Adamu ya dakatar da dukan mataimakan Inspekta da ke karkashin sa.

Akwai sani da cewa wadannan DIGs da ya dakatar sun dade ga jam’iyyar kamin zuwar Adamu, kuma sun yi aiki tare da shugaban jami’an tsaron na da, Ibrahim Idris.

 

Ku sami cikkaken labarun Najeriya a shafin Naija News Hausa