Connect with us

Uncategorized

PDP: Shin an bi doka ga tsige Alkali Walter Onnoghen – Atiku

 

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kalubalanchi shugabancin Muhammadu Buhari game da matakin da shugaban ya dauka na dakatar da babban Alkalin shari’ar kasar Najeriya, Walter Onnoghen.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da alkalin a ranar jumma’a da ta wuce, ya kuwa sanya wani maimakon sa.

Mun kuma sanar a yau da cewa sabon alkalin da aka sanya ya halarcin gidan kotun a yau don kadamar da ayukan sa a matsayin shugaba.

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana bacin ran sa da wannan mataki a shafin yanar gizon nishadin sa na twitter:

bayyanin na kamar haka:

Atiku ya ce, “Matsalar bawai ko Alkalin ya aikata laifi ne ba ko kuma bai yi hakan ba. Amma abin damuwa shi ne, shin an bi hanyar da ta dace waje dakatar da Alkalin?” wannan itace tambayar da Atiku ke yi ga shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin sa akan dakatar da Alkali Walter Onnoghen.

Ya kara gaba da bayyana murnan sa ga ‘yan Najeriya da suka tashi kai tsaye don nuna rashin amincewa da matakin shugaban kasar.

Kalli bayanin Atiku inda ya kara rattaba baki ga lamarin

Advertisement
close button