Connect with us

Uncategorized

Sabon babban Alkalin Najeriya, Ibrahim Tanko ya halarci Kotu a yau

 

Kamar yadda muka sanar a Naija News da cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Jumma’a da ta gabata ya tsige babban Alkalin Kotun Najariya, Walter Onnoghen kuma ya sanya sabon Alkali mai suna Ibrahim Tanko Muhammad.

A yayin da ake gwagwarmaya da karar Alkali Onnoghen, sabon Alkali da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar, Ibrahim Tanko ya halarci babban Kotun a yau dan kadamar da ayukan sa kamar yadda ake yi a kotun.

Ko da shike yawancin alkalai da ma’aikatan kotun su nuna irin bacin ran su da wannan matakin, sun mamaye gaban kotun da zanga-zanga don gabatar da rashin amincewan su da wannan mataki da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na dakatar da Walter Onnoghen.

Kalli bidiyon da wasu alkalai da ma’aikata suka fita zanga-zanga don nuna rashin amincewa da dakatar da CJN

Ibrahim Tanko ya halarci Kotun ne a yau Litini misalin karfe 8:00 na safiya  a yayin da kotun ta bude don kadamar da ayukansu kamar yadda ta saba.

Zaman kotun ta yau ya halarci mutane biyar ne tare da sabon babban alkalin, Ibrahim Tanko Muhammad.

Sunayen wadanda suka halarci zaman na kamar haka; Alkali Mary Peter-Odili, Amiru Sanusi, Kudirat Kekere-Ekun da Paul Galinje a yayin da suke batun kafa baki ga wasu kara da ke gaban su.

 

Ka samu karin labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Advertisement
close button