Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari ya rattaba hannu ga dokar dama ga Kamfanoni wajen tsarrafa hanyoyi a kasar

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta ruwaito da sanar da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu ga takardan dokar ‘Ba bambanci ga raggagu’ a kasar nan.

Dokar da ke tare da tarar kudi da shiga jaru ga wadanda suka karya dokar, harma hade da umurnin gine-gine da ba zai taushe hakin raggagu ba a kasar.

A yau da safiyar Litini 28, ga Watan Janairu 2019, Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu ga sabuwar dokar bada dama ga Kamfanoni masu zaman kansu don damar tsarafa hanyoyi inda ya dace a kasar Najeriya.

Shugaba Buhari ya sanya hannu ne ga takardan dokar a yau Litinin, a babban birnin tarayya, Abuja a cikin gidan Majalisar dokokin kasa ta Najeriya.

Akwai sani da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu ga wasu dokoki a baya a cikin shugabancin sa, kaman dokar ribato tattalin arzikin kasa da wasu suka sace a baya, da kuma wasu dokoki da ta kumshi ci gaban kasa da har ya kawo kiyaya da rashin yarjejeniya tsakanin shugabancin sa, Manyan shugabannan kasa da ‘yan adawa duka.

Wannan dokar zai bada dama ga kamfanoni kamar su Dangote, Un federal road silver, da Lafarge Africa da samar da hanyoyi mai kyau a kasar kuma gwamnati ta yita biyar su haraji kadan kadan.

A halin yanzun, hanyoyin Jihojin kasar Najeriya sun lallace kwarai da gaske.

“Wannan dokar zai iya sa kamfanoni da ke zaman kansu su iya samar da hanyoyi a kasar don karuwar kasa da kuma nasu biyar bukata wajen samar da ayukan kasuwancin su”.

 

Karanta kuma: Jam’iyyar PDP sun zargi shugaba Muhammadu Buhari da kasawa ga iya mulkin kasar Najeriya