Connect with us

Labaran Najeriya

Siyasa: Ku Sanya Bukola Saraki a matsayin Shugaban Kasan Najeriya – in ji Nwosu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Ga wata sabuwa: Shugaban Hukumar Dimokradiyya ta Afrika, Mista Ralphs Nwosu yayi kiran shawara ga Majalisar Dattijai da cewa su sanya shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Bukola Saraki a matsayin shugaban kasar Najeriya a gaggauce.

“Ku sanya shugaban Majalisar Dattijai a matsayin Shugaban kasar Najeriya” in ji Nwosu.

“Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa Farfesa Yemi Osibanjo ba za su iya ci gaba da jagorancin kasar nan ba, ku sanya Saraki”

Mun sanar a Naija News da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da babban Alkalin Shari’ar kasar Najeriya, Walter Onnoghen.

Bayan Buhari ya gabatar da wannan, wasu ‘yan Najeriya sun nuna bacin ran su da wannan matakin da shugaban kasan ya dauka na dakatar da Alkalin ba tare da bin hanyar da ta dace ba.

Bayyanin na kamar haka a shafin twitter:

Mun ruwaito da cewa Gwamnatin Najeriya ta jagorancin shugaba Muhammadu Buhari sun Umurci kasar United State da wasu kasashen Turai da cewa su cire bakunan su game da batun kasar Najeriya, musanman ga karar CJN, kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa ta shafin manyan labaran Jaridun Najeriya ta yau Litini , ga Watan Janairu, 2019.

Nwosu, ya gabatar da zancen sanya Bukola Saraki a matsayin shugaban Kasar Najeriya ne a wata gabatarwa da ya rattaba hannun a jiya Lahadi da aka sanar ta bakin Yemi Kolapo, Sakataren Tarayyar Hukumar ADC.

Ya ce, “Wannan mataki ce ta musanman ganin irin matakai da irin kadamarwa da shugaban kasan ke yi, musanman daukar matakai ba tare da bin dokar kasa ba irin wadda shugaba Muhammadu Buhari  ke dauka a kwanakinan. wannan ya nuna da cewa shugaban ba zai iya jagorancin kasar nan ba” in ji shi

“Shugaba Buhari bai da damar tsige babban shugaban Alkalan Tarayya ta kasar Najeriya ba tare da bin hanyar da ta dace ba kamar yadda doka ta samar. Shugaba Buhari ya ya rigaya ya aikata babban laifi ga kasar” inji shi.

 

Karanta kuma: Cutar Lassa Fever ya dauke rayuka 5 a Jihar Plateau