Connect with us

Uncategorized

APC/PDP: Kakakin Gidan Majalisar Wakilar, Yakubu Dogara yayi murabus da APC, ya koma PDP

Published

on

at

A yau Talata, 29 ga Watan Janairu 2019, Yakubu Dogara, Kakakin Gidan Majalisar Wakilai ya janye daga Jam’iyyar APC ya komawa Jam’iyyar PDP.

Muna da sani a Naija News da cewa Dogara ya dauki fam na shigar Jam’iyyar PDP shekara da ta wuce don neman takara, amma bai bayyana ga fili ba ga gidan majalisar.

Mun samu tabbaci da cewa ba Dogara ne kadai yayi murabus da Jam’iyyar APC ba amma tare da wasu ‘yan Majalisa guda biyu, Watau Ahmed Yarima daga Jihar Bauchi da kuma Edward Pwajok da Jihar Jos.

Dogara ya bayyana wannan ne a yau Talata a nan gidan majalisar, ko da shike dai ‘yan Majalisar basu bayyana dalilin da ya sa suka dauki wannan matakin ba.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Yakubu Dogara ya gabatar a ranar Litini da ta gabata a birnin Abuja da cewa Naira dubu 30,000 na sabon tsarin Kankanin Albashin Ma’aikata ya kasa ga ma’aikata ganin irin tsadar abubuwa a kasar a halin da muke ciki.

Ya kara da cewa, “Idan har ana bukatar a magance Cin hanci da Rashawa a kasar nan, dole ne a biya kudi isashe ga ma’aikata, bama kawai naira dubu talatin ba na kankanin albashi” in ji Dogara.