Connect with us

Uncategorized

Boko Haram: Gwamnan Jihar Borno, Shettima ya sanya Mafarauta ga yaki da Boko Haram

 

Yaki da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram ya zama wani babban abu ga kasar Najeriya. A koyause ‘yan ta’addan na kai hari ko ta ina duk da irin kokari da kashe su da rundunar sojojin kasar ke yi don dakatar da hare-hare a kasar Najeriya.

Gwmnan Jihar Borno, Kashim Shettima ya gabatar da cewa zai sanya Mafarauta don hakon ‘yan ta’adda a Jihar.

“Zamu sanya Mafarauta a wasu wurare cikin daji don hakon ‘yan ta’addan Boko Haram a Jihar, kuma muna kokarin ganin cewa mun samar masu da makamai da kayakin da suke bukata duka don gudanar da wannan” in ji Shettima.

Gwamnan ya gabatar da wannan shiri ne a yayin da ya ke marabtan Kwamandan rundunar sojojin ‘Operation Lafiya Dole’, Benson Akinroluyo. Ya ce “Za a samar da horo da koyarda Mafarauta kamin a kai su cikin daji don hakon ‘yan ta’addan Boko Haram” inji shi.

Naija New Hausa ta ruwaito da cewa Gwamna Kashim Shettima ya zubar da hawaye a yayin da ya ke bayani da shugaba Muhammadu Buhari a wata ganawa da suka yi a birnin Abuja wajen tattaunawa da neman mahita ga yaki da hare-haren ‘yan ta’adda ke kaiwa a Jihar. Ganawan da aka yi da Manyan shugabannan Jihar Borno.

“kwanaki kadan da nan, zamu sanya rukunin yaki da ta’addanci a Jihar, rukunin ya kumshi Mafarauta da ‘Yan Banga” in ji Gwamna Shettima.

“Mun rigaya mun samar da motoci 30 garesu don taimaka masu ga yakin kuma zamu mika su ga rundunar sojojin kasar don koya masu yadda zasu iya gudanar da aikin tsaro a Jihar, musanman yankin Maiduguri”

“Ganin zabe ya kusanto, ‘yan ta’addan zasu so su yita kai farmaki a yankin don kawar da hankalin mutane ga shirin zaben” inji shi.

 

Karanta kuma: Ku sadaukar da makaman ku, IGP na gayawa masu amfani da bindiga da ba kan doka ba

Advertisement
close button