Connect with us

Uncategorized

CAN: Kungiyar mu ba ta Siyasa ba ce – in ji Joseph Masin

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaban Kungiyar Hadin Gwuiwa ta Addinin Kiristoci na Jihar Nasarawa, Mista Joseph Masin ya fada da cewa kungiyar ba rukunin ‘yan siyasa ba ce.

Joseph ya mayar da martani ne don karyace fade-faden da ake yi na cewar kungiyar ta amince da zaben wani dan takara kujerar gwamna a Jihar.

“Mun sami rahoto da cewa wasu da ke kiran kansu shugabannan kungiyar CAN sun bi baya da karban cin hanci da rashawa daga hannun ‘yan siyasa don sayan kuri’a. Da kuma bada tabbacin karya da cewa kungiyar ta amince da jefa kuri’a ga ‘yan takaran”.

“Ba mu san da wadannan mutanen ba, saboda da haka muna kira ga ‘yan takara da su guje masu da yin hakan” in ji Mista Joseph.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa John Hayab, Kakakin Kiristocin Jihohin Arewa 19 ya ki amincewa da matsayin da Jam’iyyar PDP suka nada shi.

“Allah ne kawai ke da izinin sanya shugaba, saboda da haka na shawarci al’umma duka su san da wannan fade-faden game da kungiyar mu, ba gaskiya bane kamar yadda karyan ya bi gari”

“Kowa ya bi zuciyarsa wajen jefa kuri’a” inji shi.

Shugaban ya gabatar da wannan ne a yankin Lafiya, a Jihar Nasarawa.