Labaran Nishadi
Kannywood: Anyi Wuf da Kudin da Sanata Saraki ya bayar – Ummi Zee Zee
Naija News Hausa ta ruwaito da cewa dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar kwanakin baya ya fada wa ‘yan shirin fim da cewa idan har aka nuna masa so, kuma aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya ga zaben shekara 2019 da ke gaba, zai tabbatar da ganin cewa bai manta da bangaren nishadi ba a Najeriya .
Atiku yayi nuni ga matsaloli da ake samu a bangaren nishadantarwa, kuma yace zai magance su. Wasu daga cikin matsalolin da Atiku ya ambato na kamar haka;
- Matsalar samun isassun kudade wajen gudanar da aikace aikacen shiri
- Satar fasahar ‘yan shiri
- Sayar da ayyukansu ba tare da izinini ba
- Rashin sanin hanyoyin watsa shirye-shirye a kasuwannin duniya
- Da kuma rashin samun tallafi da sassaucin kudin wajen biyan haraji.
A yau mun sami sani a Naija News Hausa da cewa Ummi Ibrahim da aka fi sani da ‘Zee-Zee’ ta zargin wadansu sanannu da kwararrun ‘yan shirin fim a Kannywood da cewa sun yi wuf da Miliyoyin kudi da Sanata Bukola Saraki ya bayar garesu don rabawa masu shirin fim na Kannywood.
Mun sami tabbacin wannan ne a yanar gizon nishadi ta twitter da Kannywood Empire ke amfani da ita.
Sanarwan na kamar haka:
Jarumar Kannywood Ummi Zee Zee ta zargi abokan sana’arta guda 5 @sanidanja @fatymuhd zahradeen_sani, buhari_alameen da Darakta Imrana a kan cewa an yi ruf da ciki akan Miliyoyin Naira da @bukolasaraki ya ba su dan a rabawa ‘yan Kannywood masu tafiyar Dan Takara @aatiku na PDP. pic.twitter.com/cUtPBedi4h
— kannywood Empire (@KannywoodEmp) January 29, 2019
Kalla bidiyo a kasa inda aka bayyana yadda aka yi da kudaden: