Connect with us

Uncategorized

Majalisar Wakilai sun gabatar da amince da Dubu N30,000 a matsayin sabon kankanin Albashi ga Ma’aikata

 

Gidan Majalisar Wakilai a yau, Talata 29 ga Watan Janairu 2019, ta amince da kuma sanya hannu ga biyar kudi Naira dubu 30,000 a matsayin kankanin albashin ma’aikata.

Naija News Hausa ta sanar a baya da cewa Gwamnatin Tarayya ta yarda da biyan naira dubu 27,000 a matsayin sabon kankanin albashin ma’aikata. 

Ko da shike Hukumar Ma’aikatan kasa sun ki amince da 27,000 a matsayin sabon albashin, a yayin da Shugaba Kungiyar Ma’aikata, Chris Ngige ya yi barazanar cewa dole ne Gwamnatin tarayya su karasa naira dubu 3,000 da ya ragu daga naira dubu 30,000 da kungiyar su ta bukaci gwamnatin tarayya su biya tun da farko.

A yau an kai ga karshen gwagwarmayan batun sabon kankanin albashin, a yayin da Gidan Majalisa ta sanya hannu ga amince da biyar kankanin 30,000 ga ma’aikatan kasa kamar yadda kungiyar ta bukaci Gwamnatin Tarayya da shi.

Majalisar ta ce za a kadamar da sabon albashin ne ranar da Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da hakan kuma ya rattaba hannu.

Wannan ci gaba na karban kankanin albashi na naira 30,000 ya kasance ne ga ma’aikatan gwamnatin tarayya da kuma ma’aikatan Jihohi.

An kai ga wannan arjejeniya ne bayan ganawa da Majalisar ta yi a ranar Litinin 28 ga Watan Janairu, 2019 da ta gabata a birnin Abuja tare da mambobin Gidan Majalisar Dattijai da Majlisar Wakilai hade da shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kasa, Chris Ngige, da Ministan Ayuka da samar da Aiki Zainab Ahmed da kuma Yakubu Dogara, Minista kula da harkan kashe-kashen kudin kasa.

“Hukumar Ma’aikatan Kasa (NLC) ta bayyana ga Gwamnonin Jihohi talatin game da biyar naira dubu N30,000 kuma sun yarda da hakan” in ji Wabba.

Karanta kuma: Ku Sanya Bukola Saraki a matsayin Shugaban Kasan Najeriya – in ji Nwosu

Advertisement
close button