Connect with us

Labaran Najeriya

PDP: Ku Goyawa Miji na baya – inji Matar dan takaran shugaban kasa Atiku Abubakar

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Matar dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ta roki mata da su goyawa mijinta bayan don cin zaben shugaban kasa ta shekarar 2019 da ke gabatowa.

Rukayya Atiku ta yi wannan kiran ne a yayin da ta ke gabatarwa ga hidimar yakin neman zabe da a ka gudanar musanman ga matan Jihar Bauchi da ke Jam’iyyar PDP.

A yayin da ta ke gabatarwan, ta umurci matan da cewa su gucewa halin sayan kuri’u daga jama’a, kuma su tuna da ayukan da ya kamata su yi kan shirin zaben.

Rukayya ta bada wadannan sharidun ne a lokacin da ta ke gabatarwa da rarraba abinci da wasu kayaki ga matan Jihar da suka halarci hidimar a nan Bauchi.

Ta ce “Ku zabi miji na Atiku Abubakar don dakatar da rashi da yunwa, amfani da mugan kwayoyi tsakanin matasan kasar nan, da kuma samar da makarantu da tsarafa aiki dabam-dabam ga masu neman aiki a kasa” in ji ta.

Anan wajen ne kuma matar dan takaran gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar PDP, Hajiya Aisha Mohammed ta ce “Idan har PDP ta koma ga mulki, matsala zai kare ga mata da kuma matasa”.

Mun ruwaito a Naija News Hausa cewa dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana da cewa kasar Najeriya da aka sani duk Afrika da kuma duk kasar duniya da Isasshe kayan fahariyya da Isasshen tattalin arziki, harma akan yi ikirarin da cewa “Najeriya babbar Jigon Afrika, kasa mai zuba da madara, amma a yanzun nan an lisafta mu cikin layin kasa mai mumunar talaucewa a tarihi sanadiyar shugabancin APC”.