Uncategorized
Sabuwa: ‘Yan Hari da Bindiga sun sace Ciyaman na APC a Jihar Abia

Mun sami rahoto a Naija News da cewa ‘yan hari da bindiga sun sace Ciyaman na Jam’iyyar APC na Jihar Abia.
Ganin irin wannan abin bamu san abinda zai biyo baya ba ganin zaben ya gabato.
Wannan abin ya faru ne daren Litinin da ya gabata, a yayin da ‘yan hari da bindiga suka sace Ciyaman na Jam’iyyar APC na Jihar Abia, Hon. Donatus Nwankpa.
mun samu sani da cewa mataimakin ciyaman din ya samu tsira daga wannan harin, amma akwai wani daga cikin shugabannan jam’iyyar da bai tsira ba.
Duk da cewa mun sanar da safen nan a Naija News Hausa da cewa shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar Abia a yau don kadamar da hidimar yakin sake zabe.
A halin yanzun ba cikakken bayani game da wannan harin. Duk wata labari da ya biyo baya, zamu sanar a nan….
Karanta kuma: Shugaban Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ya sanya sabbin DIGs guda shidda bayan da ya dakatar da tsohin DIGs.