Connect with us

Labaran Najeriya

APC: Ziyarar shugaba Muhammadu Buhari a Jihar Abia

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tulin jama’ar Jihar Abia sun marabci shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a yayin da ya ziyarci jihar a ranar jiya, Talata 29 ga Watan Janairu 2019.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa shugaban Kungiyar ‘yan Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu ya umurci ‘yan kungiyar da cewa su zauna a gidan su a yayin da shugaba Buhari ke shirin ziyarar Jihar a ranar jiya.

Mun samu rahoto da cewa mutane sun fito makil don marabtan shugaba Buhari a Jihar wajen ziyarar yakin neman zabe da ya ka a Jihar. Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka birnin Aba ne, babban birnin kasuwancin Jihar Abia.

Wannan fitowar jama’ar ya zama abin mamaki ga Nnamdi Kannu da ‘yan kungiyar ganin irin yadda mutane suka fito makil don marabtan shugaban bayan Nnamdi Kannu ya umurci mutanen sa da ce kada su fito don marabtan shugaba Buhari a Jihar.

Ya ce, “Kowa ya zauna a gidansa a yayin da Jubril Al-Sudani da ake ce da shi Muhammadu Buhari zai ziyarci Jihar mu a yau don kadamar da mugun shirin sa na mayar da Jihar kasar Musulunci” in ji shi.

“Bari in Buhari ya shigo filin ya cinma ba kowa da ke jiran marabtan sa, saboda ba ma son shi da shirin makircin sa a jihar mu, kada kowa ya fita daga gidansa”.

Wannan shi ne umurnin da aka bawa ‘yan kungiyar IPOB da cewa kowa ya kasance gidansa a kulle daga karfe 6 na safiya zuwa karfe 4 na maraice.

Duk da hakan shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci birnin Aba don kadamar da wata Gidan Wutan Lantarki da shugabancin Buhari ta yi alkawali ga Jihar tun shekaraun baya a  nan kasuwar Ariaria da ke yankin Osisioma Ngwa, Jihar Abia. Daga nan shugaba Buhari ya haura zuwa wajen hidimar yakin neman sake zabe tare da mambobin Jam’iyyar APC nan Filin kwallon kafan Enyimba da ke anan Jihar.

Kalli yada mutane suka marabci shugaba Muhammadu Buhari a birnin Aba

Kalli kuma bidiyon shigar Shugaba Muhammadu Buhari

Ko da shike har yanzu ba wanda ya bada wata bayyani game da wannan marabtan da jama’ar Jihar suka yi daga cikin ‘yan Kungiyar Biafra (IPOB).

Karanta kuma: Majalisar Wakilai sun gabatar da amince da Dubu N30,000 a matsayin sabon kankanin Albashi ga Ma’aikata