Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba 30 ga Watan Janairu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba 30 ga Watan Janairu, 2019

 

1. Kotun NJC ta ba Onnoghen da Mohammed kwana 7 don amsa wa zargin da ake da su

Hukumar Shari’a ta kasa (NJC) ta bayar da kwana 7 ga babban alkalin Najeriya da aka dakatar, Walter Onnoghen da sabon CJN, Tanko Mohammed don amsa zargin da ake a kansu.

Mun ruwaito a Naija News da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Onnoghen a makon da ya gabata a ranar Jumma’a kuma nan da nan ya sanya Tanko Mohammed a matsayin sabon CJN.

2. Majalisar Wakilai sun amince da dubu N30,000 a matsayin kankanin albashin ma’aikatar

Gidan Majalisar Wakilai sun gabatar da zancen karin kudi ma’aikatan kasa na dubu N30,000 kamar yadda suka amince da ita a ranar jiya bayan tattaunawa da Majalisar ta yi.

Wannan ci gaban ya auku ne bayan tattaunawa tsakanin Majalisar da hukumomi da ke shawarwari akan karin kudin ma’aikatan kasa a ranar Talata da ta gabata a nan birnin Abuja.

3. Abubuwa 5 da Atiku ya ambata a yayin da yaken rokon kasar Faransi, Jamus, Birtaniya, Amurka, da EU da juyawa Buhari baya

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya wallafa wata wasika na bukatar rukunin kasashen Turai da juyawa Shugaba Muhammadu Buhari baya.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar, Atiku ya a cikin wasikar, ya zargi Buhari na karya dokunan kasa.

4. Alkali Onnoghen ya yi karar gwamnatin Buhari zuwa Kotu kan dakatarwa da aka masa

Babban Alkalin shari’ar kasan Najeriya, Walter Onnoghen yayi kirar kara ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari  game da dakatar da shi da shugaban yayi.

Shafin Farko na Naija ya ce Shugaba Buhari ya dakatar da Onnoghen a makon da ya gabata a ranar Jumma’a kuma ya sanya Tanko Muhammad a matsayin CJN. An zargi Onnoghen da ba’a bayyana dukiya ba.

Mun ruwaito a Naija News da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Onnoghen a makon da ya gabata kan zargin cewa bai gabatar da asusun sa ba ranar Jumma’a kuma nan da nan ya sanya Tanko Mohammed a matsayin sabon CJN.

5. Kakakin Gidan Majalisar Wakilar, Yakubu Dogara da wasu sun yi murabus da APC, sun koma PDP

Kakakin Gidan Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya gabatar da janyewar sa daga Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP.

Dogara ya sanar da wannan matakin ne ga Majalisar a ranar Talata da ta gabata a wata ganawa da Majalisar ta yi a birnin Abuja.

Mun samu tabbaci da cewa ba Dogara ne kadai yayi murabus da Jam’iyyar APC ba, amma tare da wasu ‘yan Majalisa biyu, Ahmed Yarima daga Jihar Bauchi da kuma Edward Pwajok daga Jihar Jos.

6. Shugaban ‘Yan sanda, IG Mohammed Adamu ya gana da NSA tare da gwamnonin jiha

Babban Jami’in Tsaro na ‘yan sanda, Mohammed Adamu da kuma Babban Mashawarcin Tsaro na kasa, Babagana Monguno sun gana da gwamnonin jihohi a Abuja ranar Talata da ta gabata.

An gudanar da taron ne don tattaunawa ga matsalolin tsaro da kuma yadda za a magance su kamin zaben tarayya da ke gaba.

7. Biafra ta sanya ranar 16 ga watan Fabrairun, rana daya ga zaben kasa don kadamar da kasar Biafra a Najeriya

‘Yan kungiyar Biafra (IPOB) sun bayyana ranar 16 ga Fabrairu, 2019 a matsayin sabon ranar da za su raba nasu jiha daga kasar Najeriya.

Ranar ta zama daya da ranar da kasar Najeriya zata gabatar da sabon shugaban kasa da zai hau mulki bayan zabe.

8. Gwamnatin tarayya ta fito da sabbin zargi kan Walter Onnoghen

Ofishin Babban mai Yanke Shari’ar Tarayya ya aika da jerin sabbin zargi akan Alkali Water Onnoghen da aka dakatar.

Ya gabatar da zargin ne ga Hukumar Alkalan Kasa. Zargin ta kumshi laifin rashin gabatar da asusun kudin sa da kuma zargin wasu dukiya da aka gano a sunan Alkali Walter Onnoghen.

9. Yan Hari da Bindiga sun sace Ciyaman na APC a Jihar Abia kamin isowar Buhari

Wannan abin ya faru ne daren Litinin da ya gabata, a yayin da ‘yan hari da bindiga suka sace Ciyaman na Jam’iyyar APC na Jihar Abia, Hon. Donatus Nwankpa kamin isowar shugaba Muhammadu Buhari a Jihar.

mun samu sani da cewa mataimakin ciyaman din ya samu tsira daga wannan harin, amma akwai wani daga cikin shugabannan jam’iyyar da bai tsira ba.