Connect with us

Uncategorized

PDP: Dakali ya tsinke da ‘yan Jam’iyyar PDP a wajen ralin zabe a Jihar Kebbi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Ana wata- ga wata: Yan Jam’iyyar PDP sun fadi daga kan Dakali a wajen hidimar rali da Jam’iyyar ta gudanar a Jihar Kebbi.

Wannan abin ya faru ne a yankin Jeda, anan Jihar Kebbi ranar Litinin da ta gabata a yayin da Jam’iyyar ke gudanar da hidimar ralin yakin neman zabe a Jihar.

“Dakalin ya fadi ne da ‘yan siyasan, harma sun zube a kasa dukansu a yayin da daya daga cikin su ke gabatarwa a akan dakalin”.

Mun samu sani a Naija News da wannan faruwan inda aka nuno taron ‘yan Jam’iyyar PDP akan dakali a yayin da guda cikin su ke gabatarwa kamin dakalin ta tsinke da su.

Kalli abin cikin wannan bidiyon

A halin yanzun, wannan bidiyon ta bi ko ta ina a yanar gizo.

An iya gano Isah Muhammad Galaudi, dan takaran Gwamnan Jihar Kebbi na Jam’iyyar PDP tare da sauran mambobin Jam’iyyar a wajen da abin ya faru.

 

Karanta kuma: Shaharar ‘yar wasan fim na Hausa, Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta zargi wasu daga cikin manyan ‘yan shirin fim din Kannywood da cewa sun yi Wuf da Kudin da Sanata Saraki ya bayar don a raba wa masu shirin fim.