Connect with us

Uncategorized

Sabuwa: An kara sace wani Ciyaman na Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa

 

Mun samu rahoto yanzun nan a Naija News Hausa da cewa an sace ciyaman na Jam’iyyar APC na yankin Demsa, Jihar Adamawa.

Bayan wasu hare-hare da ‘yan ta’adda suka yi na sace ciyaman na Jam’iyyar APC a Jihar Abia a yayin da shugaba Muhammadu Buhari ke batun ziyarar Jihar a ranar Talata da ta gabata.

Mun sami sabuwar rahoto da cewa ‘yan hari da bindiga sun sace Hamisu Mijinyawa, Ciyaman na Jam’iyyar APC a yankin Demsa, Jihar Adamawa.

Wannan mumunar harin ya faru ne a misalin karfe 1 na safiya ta ranar yau Laraba 30 ga Watan Janairu, 2019 a gidan sa a yayin da Jam’iyyar ke shirin gudanar da hidimar yakin neman zabe a yankin Demsa, kamar yadda manema labaran Sahara suka bayar kuma.

“Maharan su sace shugaban Jam’iyyar ne yau da safiya a gidan sa, misalin karfe 1 na safiya. sun kuma bukaci a biya kudi kimanin Miliyan ashirin (N20m) kamin dada su sake shi” in ji Mark Dauda, daya daga cikin shugabannan Jam’iyyar APC a nan yankin.

“Sun yi kira, kuma sun bukaci a biyar kudi kimanin naira Miliyan 20 kamin su sake shi” inji shi.

‘Yan hari da bindiga sun sace Donatus Nwankpa ne da dare a gidan sa.

Mai yada labarai ga ‘yan sandan Jihar, Geoffrey Ogbonna ya bayyana da cewa Jami’an tsaron na bincike da shirin gaggawa don ribato ciyaman din, da kuma kame ‘yan ta’addan da suka aikata irin wannan abin.

Advertisement
close button