Uncategorized
Zaben 2019:

Jam’iyyar APC ta sanarwa mambobin ta da magoya bayan Jam’iyyar a Jihar Kano da cewa hidimar rali na yakin neman zaben shugaban kasa na Jam’iyyar zai kasance ne a ranar Alhamis da ke gaba.
kamar yadda muka sani da cewa zaben shugaban kasa da zaben tarayya ta gabato, Jam’iyyar APC na gudanar da yawon yakin neman zabe a kowace jiha kamar yadda sauran Jam’iyun su ma ke gudanar da tasu.
Jam’iyyar ta sanar da hakan ne a shafin nishadarwar twitter na su.
Ga sanarwan kamar haka;
This is to inform all our party faithful and supporters in Kano State that the Presidential Campaign Rally will hold Thursday, January 31, 2019 as originally scheduled. — APC PCC’s @fkeyamo pic.twitter.com/foKrHzQqNU
— APC Nigeria (@APCNigeria) January 30, 2019
A halin yanzu muna da sani a Naija News da cewa shugaba Muhammadu Buhari na a Jihar Ebonyi wajen hidimar yakin neman zabe.
Rahoto akan wannan zai biyo daga baya…..