Connect with us

Uncategorized

Ka bayar da Bakasi ga kasar Cameroon, ba zamu yafe maka ba, Oshiomole ya cewa Obasanjo

 

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya bayyana yadda tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayar da Bakasi ga kasar Cameroon a shekarun baya.

“Jama’ar Najeriya ba zasu gafarta maka ba da matakin da ka dauka na bayar da birnin Bakasi ga kasar Cameroon don kana nemar farantawa kanka”

Wannan shi ne fadin Adams Oshiomole ga Obasanjo game da matakin da tsohon shugaban kasar ya dauka shekarun baya da suka shige.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Yan Najeriya sun Mamaye Birnin Abuja da zargin Obasanjo da halin Makirci da Kulle-kulle tashin hankali a kasar, harma sun bukaci gwamnati da kame shi.

“Tahiri za ta ci gaba da tsine maka, Najeriya ba za ta yafe maka ba”

Adams Oshiomhole ya fadi hakan ne a birnin Calabar, nan Jihar Cross Rivers wajen hidimar yakin neman sake zabe ga shugaba Muhammadu Buhari a Jihar.

Inda ya fada da cewa Obasanjo ya bayar da Bakasi ne ga kasar Cameroon don faranta wa ransa da kuma neman girma.

“Ka raba Miji da Matar sa, ka raba mutane da ‘yan uwansu, Idan ma ba mu iya horan ka ba, Tarihi zata ci gaba da horon ka” inji shi.

Ka tuna da cewa, makon da ta wuce Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana a wata ganuwa da manema labaran BBC da cewa dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya fi Buhari kirki har so biyu.

Obasanjo ya ce “Kowa na iya satar tattalin arzikin kasan nan kuma ya tsira idan har dan Jam’iyyar APC ne shi”.

Adams Oshiomhole ya karshe da cewa Allah zai yi aikin sa ga zaben tarayya da ke gaba, kuma Allah zai hori Obasanjo da wanda ya ke mara wa baya ga takara.

Advertisement
close button