Connect with us

Uncategorized

Kannywood: Rikici ta barke tsakanin ‘yan shirin Fim na Hausa

 

Babban rikici ya barke tsakankanin ‘yan shirin fim na Kannywood

Ana wata ga wata: ‘yan shirin fim na Kannywood sun yi barazanar kai kansu kara a kotu sakamakon kudi da ‘yan takara suka raba masu.

Ummi ZeeZee da Zaharaddeen Sani sun yi barazanar kai karar junan su akan kudi da aka bawa ‘yan kungiyar don kadamar da yakin neman zabe.

Mun sanar a Naija News Hausa ‘yan kwanaki da nan da cewa Ummi Ibrahim da aka fi sani da Zee-Zee ta zargi wasu manya daga cikin masu shirin fim na Kannywoood da cewa sun yi wuf da kudin da Sanata Bukola Saraki ya raba wa kungiyar.

Naija News Hausa na da sanin cewa kungiyar ‘yan shirin fim na Hausa (Kannywood) ta rabu biyu a wannan lokacin akan zaben shugaban kasa ta shekarar 2019, dalilin kuwa itace, wasu daga cikin kungiyar na goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari ga zabe na gaba, wasu kuma ra’ayin su na ga dan adawar Buhari, watau Alhaji Atiku Abubakar dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP.

Wannan itace sanadiyar rabuwar Kannywood ga ‘yan takara biyu.

Mun kuma samu sani da cewa wata rukunin daga cikin Kannywood sun yi ganawa da Jam’iyyar PDP game da zancen yakin neman zabe.

Acikin rukunin mu ka samu sunayen mutane kamar; Sani Danja, Al’amin Buhari, Fati Mohammed, Zaharadden Sani, Imraanaa Mohammed, da Yakubu Mohammed da suke taimakon Alhaji Atiku Abubakar don kadamar da shirin yakin neman zabe.

Rukunin sunyi ganawa ne a ranar Asabar da ta gabata, 26 ga watan Janairu, 2019. Inda mambobin PDP a jagorancin Bukola Saraki suka tattauna akan yadda zasu tafiyar da hidimar yakin neman zabe ga zaben 2019 da ta gabata.

Rahoto ta bayyar da cewa a karshen ganawar, Bukola Saraki da ya wakilci Alhaji Atiku Abubukar wajen ganawar, ya bawa kungiyar kudi don su yi amfani da shi wajen gudanar da hidimar yakin neman zabe.

Bayan wannan ganawar ne Zee-Zee ta tayar da murya tsaye cewa dole ne ita ma a sallame ta.

Bayan jayayyan hakan tsakanin ta da Zaharaddeen shi ne Ummi ta aika a shafin nishadin ta da cewa “Wasu sun yi wuf da kudin da aka raba masu a shafin Kannywood”, kamar yadda Naija News Hausa ta sanar.

“Ina da tabbacin cewa an bamu kudi mu raba amma wasu sun yi wuf da shi” in ji Ummi.

“Ba don tsohuwata da ta ce kada inyi hakan ba, daman ina da muradin in yi karar ku duka a kotu” inji ta.

“Zaharadden Sani ya kira ni kuma ya aika mani da kudi naira N25,000, to bari in tabbatar masu da cewa ni ba maroka ba ce, nafi karfin naira dubu 25,000 da ya aiko mani da shi”

“Idan har irin wannan zarafin ya kara tasowa kuma kuka yi mini haka, to lallai zan nuna maku ko ni wacece” inji ta.

Da manema labaran Premium suka binciki Zaharadden Sani, da ake kira da shi ‘Sarkin Yakin Atiku’ akan abin da ya faru, Zaharadden ya bayyana duk abin da ya faru kuma ya iya nuna da cewa lallai an bayar da kudi bayan tattaunawar da suka yi da manyan Jam’iyyar PDP a jagorancin Sanata Bukola Saraki da ya wakilci Alhaji Atiku Abubakar.

“Kuma ina tabbatar maku da cewa Ummi ba ta cikin kungiyar ta mu, bamu taba ganin ta ba ko sau daya” in ji Sani.

“Da ta kira ni game da kudin da aka bayar, na iya bayyana mata da hakan kuma da na ga cewa tsanin yayi yawa, sai na aika mata da naira dubu 25,000 daga aljihu na, bama daga kudin da aka bayar ba”

“Kawai dai ZeeZee barazana take don bata da wani muhinmanci da kuma wata karuwa a shafin Kannywood kuma” inji Zaharadden.

“Na kuma gabatar da wannan ga Jami’an ‘Yan Sanda tun da wannan naciyar nata ya fara”

Karanta wannan kuma: Kungiyar Mallaman Makarantar Sakandiri sun bukaci gwamnatin Najeriya da dakatar da shirin sanya ma’aikatan N-Power don sanya kwararrun Mallamai a makarantu.

Advertisement
close button