Uncategorized
Kishiya: Mijina ya duke ni don bai gayar da kishiyata ba – inji Zainab

Wani mutumi yayi wa matarsa duka wai don bata gaida kishiyarta ba
Oare Abdulrazak, wani mutumi da ke da mata Ukku ya duki gudar da ake ce da ita Zainab Ahmed, wai don bata gayarda kishiyarta ba.
Mun sami rahoto a Naija News Hausa da cewa Zainab Ahmed ta yi karar mijin na ta a wata Kotun shari’a a yankin Magajin Gari, nan Jihar Kaduna da zargin cewa maigidansu yayi mata duka kan cewa bata gayarda kishiyarta ba.
Zainab ta bayyana wannan ne ga kungiyar manema labaran Najeriya (NAN) da cewa maigidan nata ya duke ta ne wai don bata gayarda kishiyarta ba a lokacin da suka hade a kasuwa.
Zainab Ahmed da ke zama a Hayin Dan-Bushiya ta bayyana da cewa ba farkon mijin ta kenan ba da dukarta, yayi hakan kusan sau ukku, “A wannan lokaci na bukace shi da bani daman bayyana abin da ya faru amma bai saurareni ba” in ji ta.
Da aka bukaci Abdulrazak da bayyani, ya ce “Wannan shine kawai farkon bugun da nayi mata, kuma tun lokacin da na aikata wannan, na gane kuskuren da nayi, kuma na roke ta” inji shi.
Ko da shike, Zainab ta bayyana wa kotu da cewa maigidan nata bai nuna mata kulawa ko kadan, musanman ace ma ya shiga dakin ta.
“Ina bukatar ma a raba mu da auren nan, na gaji da hakan” inji Zainab.
Malam Musa Sa’ad-Goma, Alkalin da ke shari’ar ya bukacesu da kowa ya kawo waliyin sa a zaman kotun ta ga. Ya kuma daga karar har zuwa ga ranar 11 ga watan Fabrairun, a shekara ta 2019.
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa wani mutum da ake kiran sa Abdullahi Yadau ya ba wa matarsa sakin aure har biyu don matar ta bayyana da cewa zata zabi shugaba Muhammadu Buhari ga zaben 2019.