Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis 31 ga Watan Janairu, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis 31 ga Watan Janairu, 2019

 

1. APC ba za ta yi takara a Jihar Zamfara ba – INEC

Hukumar gudanar da zaben kasar Najeriya INEC sun nace da cewa Jam’iyyar APC ba zata yi takarar zabe ba a Jihar Zamfara.

Hukumar ta sanar da wannan ne a ranar Laraba da ta gabata bayan ganawar hukumar. Hukumar ta nace da wannan matakin na su da cewa tun da Jam’iyyar bata gudanar da zaben firamare ba a hanyar da ta dace, lallai Jam’iyyar ba za su yi takarar zabe ba a Jihar, musanman takaran Gwamna da kuma gidan Majalisar Dattijai.

2. A ƙarshe Hukumar EFCC tayi karar Babachir Lawal zuwa kotu

Hukumar Kulawa da Tattalin Arzikin kasa da Jarinta (EFCC) ta kaddamar wasu lamuni 10 kan tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal.

Mun bayar da wannan a sanin Naija News da cewa hukumar ta kai wannan karar ne a Kotun koli na babban birnin tarayya kasa, Abuja.

3. Atiku ya amince ya ba da amsar ga masu tayar da kayar baya idan an zabe su

Kwamishinan ‘yan takarar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce zai yi la’akari da bayar da amnesty ga masu ba da rancen kudi na Najeriya wanda ke son mika wuya ga hannunsu.

Rahotanni na Naija sun nuna cewa dan takarar shugaban kasa na PDP ya yi wannan sharhi yayin da ya gabatar da ‘yan takara a kan shirye shiryen talabijin a zaben shekarar 2019 wanda Kadaria Ahmed ya kafa.

3. Zan yi afuwa ga wadanda suka sace tattalin arzikin kasa idan har sun tuba – Atiku

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana da cewa zai bada afuwa ga wadanda suka sace arzikin kasa idar har sun bayyana tubarsu kuma suka mayar da kudaden da suka sace.

Dan takaran ya gabatar da wannan ne a wata ganawa da shi da abokin takaran sa, Peter Obi suka halarta a gidan talabijin da Kadaria Ahmed ta jagoranta kan wata liki ‘Dan Takara’ da aka gudanar a ranar Laraba da ta gabata.

4. Kotun tayi watsi da bukatar Onnoghen ta dakatar da karar shi

Kotun koli sun ki amincewa da bukatar babban alkalin Najeriya, Walter Onnoghen akan cewa ya bukaci kotun ta dakatar da gwajin da ake yi a kansa.

Kotun sun bayyana hakan ne a zamar da suka yi a ranar yau, anan birnin Abuja.

Mun ruwaito a Naija News da cewa alkali Walter Onnoghen ya wallafa wasika ga kotu na bukatar cewa kotun ta dakatar da gwajin da ake masa.

5. Na arawa hukumar EFCC kudi Miliyan N300m don su fara aikinsu – inji Atiku

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana da cewa ya baiwa Hukumar EFCC tallafin kudi Naira Miliyan Dari Ukku (N300) a lokacin da hukumar ke shirin kafa rukunin ta a baya.

Alhaji Atiku Abubakar, Dan takaran shugaban kasan ya gabatar da wannan ne a wata ganawa da shi da abokin takaran sa, Peter Obi suka halarta a gidan talabijin da Kadaria Ahmed ta jagoranta kan wata liki ‘Dan Takara’ da aka gudanar a ranar Laraba da ta gabata.

6. Mutane 2 sun mutu, motoci sun kone a fashewar motar man fetur a Jihar Legas

Wata mumunar hadari ta auku a babban hanyar Badagry, Jihar Legas inda wata motar tanki dake dauke da man fetur ta fashe.

An samu tabbacin cewa mutum biyu sun mutu a sanadiyar hadarin. motar da ke dauke da man fetur na kimanin lita 33,000 ta fashe ne a hanyar Badagry a wata masaukar mota na zuwa barikin sojoji nan Jihar Legas.

Masu shaida sun ce lamarin ya faru ne a misalin karfe 5 na safiyar ranar Laraba.

7. ‘Yan hari da bindiga sun sace Ciyaman na Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa da neman fansa na Miliyan N20m

Mun sami sabuwar rahoto da cewa ‘yan hari da bindiga sun sace Hamisu Mijinyawa, Ciyaman na Jam’iyyar APC a yankin Demsa, Jihar Adamawa.

Wannan mumunar harin ya faru ne a misalin karfe 1 na safiya ta ranar Laraba 30 ga Watan Janairu, 2019 a gidan sa a yayin da Jam’iyyar ke shirin gudanar da hidimar yakin neman zabe a yankin Demsa, kamar yadda manema labaran Sahara suka bayar kuma.

8. Atiku na kokarin faranta ran ‘yan kasashen waje ne kawai – inji Oshiomhole

Shugaban Jam’iyyar APC na tarayya, Adams Oshiomhole ya yi zargin cewa dan takaran Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar na aiki ne don faranta ‘yan kasashen waje.

Ya ce bayyana hakan ne a hidimar yakin neman zaben shugaban kasa na Jam’iyyar APC wanda aka yi a filin wasa na garin Abakaliki a Jihar Ebonyi.

9. Kungiyar musulunci, JIBWIS zata gana da Buhari da kuma Atiku a birnin Abuja

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar za su halarci wata taro na kungiyar musulummai da ake ce da ita ‘Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah, JIBWIS’ a birnin Abuja.

An sanar da cewa taron zai kasance ne a ranar Lahadi a birnin Abuja inda za a kadamar da wata bukatar kudi don sayan kayakin da zai taimaka ga samar da Ilimin Fasaha.

10. Kamfanin Coca-cola sun saye kamfanin Chi limited

Mun sami rahoto a Naija News Hausa da cewa Kamfanin Cola-Cola ta saye Kamfanin Chi Limited.

An sanar da wannan ci gaba na Kamfanin Coca-Cola ne a ranar yau 31, Alhamis ga Janairu, 2019. Kamfanin ta yi wannan ne don kara bunkasa hanyar kasuwancin su.

 

Samu cikakkun labaran Najeriya a shafin gidan labaran Naija News Hausa

Advertisement
close button