Connect with us

Uncategorized

Zaben Jihar Kaduna: Ban damu ba ko da na fadi ga zabe na gaba – inji El-Rufai

Published

on

at

advertisement

Gwamnar Jihar Kaduna, Nasir el-Rufai ya bayyana da cewa bai damu ba ko da ace bai ci zaben takaran gwamnar Jihar Kaduna ba ga zaben tarayya da ke gaba, “Idan har an gudanar da zaben  a hanyar da ta dace” inji shi.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa, Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna ya ce, Ko da ya sanya Paparoma ne a matsayin abokin takaransa, Kristocin Kaduna ba za su zabe shi ba.

El-Rufai ya ce babban abin muhimanci gareshi ita ce ganin cewa an gudanar da zabe mafi kyau da kwanciyar hankali a Jihar.

Gwamnan ya bayyana wannan ne a ranar Laraba da ta gabata a yayin da ya ke gabatarwa a wata zama na zamantakewar Jiha da aka gudanar a Jihar.

“Bari in bayyana maku da cewa bukata ta itace samar da shugabanci da ya dace a Jihar Kaduna” inji shi.

“Ba matsala ba ne koda ban chi zabe na gaba ba, amma abin muhimanci itace ganin cewa mun cika alkawalin mu kamar yadda muka bayar ga Jihar a lokacin da aka zabe mu ga mulkin Jihar. Idan mun lashe zabe na gaba Alhamdulillahi sai mu ci gaba da aikata ayukan mu, Idan kuma muka fadi zaben, ba matsala ba ce” in ji El-Rufai.

“Zamu ci gaba da rayuwar mu kamar yada take, Siyasa ba dole ba ce, shi yasa muka sanya hannu ga takardan zamantakewar kasa. Idan dai lallai an gudanar da zaben a hanyar da ta dace, zamu dauki hasara”

 

Karanta wannan: Jam’iyyar PDP sun ce ba wanda ya ji mugun rauni a faduwar Dakali da ya auku a Jihar Kebbi