Uncategorized
An saki Donatus, Ciyaman na APC da aka sace a Jihar Abia

Ciyaman na Jam’iyyar APC a Jihar Abia, Donatus Nwankpa da muka sanar a Naija News Hausa kwanan baya ya samu yancin sa.
Mun sanar a baya da cewa an sace Donatus a Jihar Abia a gidansa da dare, ‘yan awowi kadan da ziyarar shugaba Muhammadu Buhari a Jihar.
Mun sami tabbacin yancin sa ne kamar yadda aka bayar a gidan Jaridar ‘Punch’ da cewa an saki Donatus a daren Alhamis da ta gabata.
“Bamu biya ko taro ba don samun yancin sa, kamar yadda ‘yan hari da bindigan suka bukace mu da hakan” in ji Benedict Godson, sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Abia.
“Abin godiya ne ga Allah da wannan yancin, mun kuma gode wa duk wadanda suka bada goyon baya da kuma taimakawa wajen ganin cewa Ciyaman din ya samu yanci daga hannun ‘yan harin”
“Musanman ma, mun gode wa dan takaran Gwamnar Jam’iyyar mu na Jihar Abia da na shi irin kokarin da goyon baya wajen ganin cewa Donatus ya samu yanci” inji Benedict.
Kwamishanan Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Jihar Abia, Chris Ezike, ya bada tabbacin wannan yancin na Donatus.
Karanta kuma: Wani mutumi yayi wa matarsa duka wai don bata gaida kishiyarta ba