Connect with us

Labaran Najeriya

#BabaYaKasa: Ba mu son ka kuma, ‘yan Najeriya sun gayawa Buhari

Published

on

at

Yau sauran kwana goma sha biyar 15 da soma zaben tarayyar kasar Najeriya, amma ‘yan Najeriya sun mamaye yanar gizo da likin #BabaYaKasa.

Ko da shike muna da sani a Naija News Hausa da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya samu marabtan jama’a makil a ko ta ina da ya shiga a kasar don hidimar yakin neman zabe, har ma sanadiyar yawar mutane ya sa wasu sun rasa rayukansu a hidimar yakin neman zaben a wasu Jihohin kasar Najeriya da Buhari ya ziyarta, kamar yada muka sanar a baya.

Yau 1 ga watan Fabrairu, kwana 15 da fara zaben tarayya, ‘yan Najeriya sun mamaye hanyar nishadarwa ta twitter don bayyana ra’ayin su ga zaben 2019.

Na farkon na dauke da bayyanin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, inda tsohon shugaban ya ce “Mumunar abu a tarihin kasar Najeriya itace, Gwamnati ta bayan shugabancin shekaru 4 ta dawo da nuna mana yatsu takwas 8. Watau alamun sake komawa ga mulki, maimakon mu ga ayuka ta kwarai, sai yatsu 8 ake daga wa a sama kaman ta kutare. Wannan alamar kuturci ce, Dole ne mu kawar da wannan a kasar mu” inji fadin Obasanjo a wata sako da ya wallafa kwanakin baya.

Bayanan na su na kamar haka:

https://twitter.com/Reubenoscar1/status/1091208759010037760

Duk da hakan, Akwai alamu da cewa shugaba Muhammadu Buhari na samun goyon baya da gaske, kamar yadda muka sanar a baya da cewa wasu Kwararrun ‘yan shirin fim na Hausa (Kannywood) sun halarci hidimar yakin neman zaben da shugaba Buhari ya je a ranar Jiya, a Jihar Kano.

 Advertisement
close button