Connect with us

Uncategorized

Makiyaya sun kashe wani ASP na Jami’am ‘Yan Sanda a Jihar Delta

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mun samu sabuwar rahoto yanzunan da cewa wasu Makiyaya sun kashe wani ASP na Jami’an tsaron ‘Yan Sanda a Jihar Delta.

Abin ya faru ne a yayin da ASP din da sauran jami’an tsaron ke zagayar daji don kame wasu makiyaya da ake zargin su da sace-sace mutane a nan yankin Ndokwa ta Jihar Delta.

Ko da shike ba a ambaci sunan ASP din ba, amma an bayyana da cewa bai dade ba da aka kai shi rukunin ‘yan sandan Ashaka, anan yakin. Ya jagoranci wasu ‘yan uwansa ‘yan sanda ne zuwa cikin daji don neman kame ‘yan ta’addan makiyayan da ake zargin su da halin sace-sacen mutane a Jihar. Suna cikin yin hakan ne aka samu rahoto da cewa makiyayan sun fado masu da harbe-harbe da har alsashin bindiga ya fada wa ASP din.

“An kashe ASP din ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu, 2019 a yayin da suke zagayen nemar kame makiyayan da ake zargi” in ji Mista Andrew Aniamaka, Sakataren yada labarai ga Jami’un tsaron Jihar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa wasu ‘Yan Hari da bindiga sun Kashe Insfektan ‘Yan Sanda biyu a kauyen Magaji, Jihar Katsina kwanakin baya.

Rahoto ta bayar da cewa ‘Insfektan biyu da aka sani da suna, Bashir da kuma Ibrahim sun shiga tsaron kauyen ne sakamakon kiran tsaron da jama’ar kauyan suka bukaci yankin da shi kan irin hari da mahara ke kai masu.

“Mun samu rahoto ne da cewa wasu makiyaya sun sace wani, daga nan muka tura jami’an tsaro don neman kame ‘yan ta’addan. Suna kan dawowa ne makiyayan suka fada masu da harbi har harsashin bindiga ya fada wa ASP din” inji kakakin yada yawun jami’an tsaron Jihar.

Ko da shike Ofisan bai gabatar da sunan ASP din da aka harbe ba, da cewa iyalansa basu san da lamarin ba tukunna.

“ASP din ya mutu ne a Asibiti a ya yin da ake nuna masa kulawa. mun rigaya mun aika jami’an tsaro a dajin tare da wasu ‘yan banga don ganin cewa an kame masu aikata irin wannan mumunar abin” inji Aniamaka.

Mun ruwaito a Naija News da cewa Gwamnan Jihar Borno, Shettima ya ce zasu sanya Mafarauta cikin daji don yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram a Jihar.