Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 1 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 1 ga Watan Fabrairun, 2019

 

1. Ba mara gaskiya da zai tsira a karkashin Buhari – inji Shugabancin kasa

Farfesa Bolaji Owasanoye, Sakataren Kwamitin Shawarwari ga Shugaban kasa kan Cin Hanci da Rashawa (PACAC), ya bayyana da cewa mutanen da suka sace kudi ko kuma dukiyar kasar Najeriya ba su da wani wurin ɓuya a karkashin shugabancin Shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan shi ne bayyanin Farfesa Bolaji a gabatarwan wata takarda da ya yi a wajen taron da suka yi a birnin Legas ranar Alhamis da ta gabata.

2. Jam’iyyar APC sun mayar da martani akan muhawarar dan takara da Atiku/Obi suka halarta

Jam’iyyar sun kafa baki ga batun muhawarar tseren dan takaran shugaban kasa da Atiku Abubakar da abokin takaran sa Peter Obi suka halarta a wata gidan talabijin ranar 31 ga wata Janairu, 2019.

“Bayanin su wajen muhawarar duk karya ce” inji cewar Barrister Festus Keyamo da cewa duk abin da Atiku da mataimakin takaran sa suka fada karya ne duka.

3. Amaechi ya kalubalanci Peter Obi da gasar muhawar

Jagoran hidimar takaran Shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Rotimi Amaechi ya kalubalanci abokin Peter Obi, abokin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP da gasar muhawara ta fili.

Amaechi ya bayyana a wajen hidimar yakin neman zaben Jam’iyyar su da cewa zancen Peter Obi a wurin zaman muhawarar da suka yi a jagorancin Kadaria Ahmed, da cewa duk karya ce.

4. CCT ta dakatar da gwajin Onnoghen har zuwa ranar 4 ga watan Fabrairu

An dakatar da gwajin da ake wa babban alkalin kotun Najeriya, Walter Onnoghen har zuwa ranar Litinin, 4 ga watan Fabrairun a shekara ta 2019.

Kakakin yada yawun Kotun, Ibrahim Al-Hassan ya bayyana a ranar Alhamis da ta gabata da cewa an dakatar da gwajin da ake wa alkalin har zuwa ranar Litinin ta gaba.

5. Ba ja dabaya ga yajin aiki – Hukumar JOHESU sun nace da hakan

Hadaddiyar Kungiyar Harkokin Kiwon Lafiya (JOHESU) sun gabatar da shirin su na komawa ga yajin aiki da kungiyar ta soma yi a kwanakin baya.

Muna da sani a Naija News da cewa kungiyar ta dakatar da yajin aikin da suka fara a watan Mayu ta shekarar 2018. A halin yanzun kungiyar na barazanar cewa zasu komawa yajin aikin idan har gwamnatin tarayya bata cika arjejeniyar su ba ga kungiyar.

6. Nnamdi Kanu ya bayyana dalilin da kungiyar IPOB zata kauracewa zaben Najeriya

Shugaban kungiyar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya ce dole ne mambobinsa su kauracewa zaɓen tarayyar  Najeriya saboda wannan ita ce “lokaci mafi kyau da tsige shugabannai marasa adalci” in ji shi.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa kungiyar IPOB ta umurci mambobinta da cewa kada su fita ga marabtan shugaba Muhammadu Buhari a ziyarar da shugaban kai wa Jihar Abia.

7. Abin da Gwamnatin tarayya zata yi wa Onnoghen – Farfesa Osibanjo

Rukunin Alkalan Najeriya goma sha biyu 12 sun gana da Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo akan rikice-rikicen gwajin da ake yi wa babban Alkalin Shari’ar Najeriya, Walter Onnoghen.

Sun yi ganawar ne a Fadar Shugaban kasa don neman sauki ga karar CJN.

8. Farfesa Wole Soyinka ya bayyana ra’ayin sa ga zaben shugaban kasa

Sanannen marubuci, Farfesa Wole Soyinka ya gabatar da ra’ayin sa ga shugabancin Najeriya a wata ganuwa.
Farfesan ya bayyana da cewa ba zai mara wa dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ba ko shugaba Muhammadu Buhari da ke takaran kara komawa ga mulki.

“Lokaci yayi da rawa zata canza” inji shi.

Wole Soyinka ya gabatar da wannan ne awata tattaunawa da ake gudanar a yau da Farfesan ya halarta.

9. Bukola Saraki ba zai ci zabe ba balai ya koma matsayin Shugaban Majalisar Dattijai – APC

Jam’iyyar APC sun sake kafa baki ga batun Sanata Saraki da cewa ba zai ci zabe ba balai ma ya koma matsayin sa na shugaban majalisar dattijai, don ya janye daga jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar adawar su, PDP.

Sun yi bugun gaba da cewa shugaban Majalisar Dattijan ba zai ci nasara ga zabe na gaba ba, sun bada gaskiya cewa ko a Jihar Kwara ma sai mutanen sa sun kada shi ga zabe.

10. An daga gwajin Shari’ar Evans har zuwa ranar 6 ga Fabrairu

An dakatar da karar da ake da shahararen shugaban masu sace mutane, da aka fi sani sa da sun EVANS, sanadiyar rashin bayyanar dan Sanda Idowu Haruna, wani jami’in ‘yan sanda da kuma mai shaida ga zargin da ake wa shahararen shugaban masu satar mutanen, EVANS.

Evans da sauran rukunin sa zasu bayyana a gaban kotun kara kan zargin kashe wani ciyaman na ‘The Young Shall Grow Motor da ake ce dashi Vincent Obianodo.

Ka sami karin bayanai ga labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Advertisement
close button