Connect with us

Uncategorized

Zaben 2019: Akwai tashin hankali idan aka yi Makirci ga zaben 2019 – Uche

 

Shugaban Jam’iyyar PDP na tarayya, Uche Secondus yayi barazanar cewa akwai tashin hankali a kasr idan har Jam’iyyar APC ta nuna makirci ga zaben shugaban kasa da ya gabato.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Shugaban Hukumar kadamar da Zaben Kasan Najeriya (INEC)Mahmoud Yakubu a baya, ya bayyana da cewa hukumar INEC ba zata juyewa amincin da take da shi ba don wata tsanani ko damuwa daga ‘yan takara ko Jam’iyyar su.

Uche Secondus ya gargadi Hukumar INEC da cewa kada su kuskura su yi makirci ga zaben tarayya da ke gaba.

“Mun gargadi Hukumar INEC da cewa kada su yi makirci ga zaben 2019, ko da shike mun san da cewa akwai masu adalci cikin hukumar, kuma muna da sani cewa gwamnatin kasar na tsananta wa hukumar da yin makirci. Za a yi tashin hankali a kasar nan idan har hakan ya faru” inji Uche.

“Idan har an son kwanciyar hankali a kasar, lallai na gargadeku da adalci ga zaben 2019, ko kuma a tada tanzoma”

Uche Secondus ya gabatar da wannan ne a ranar 31 ga watan Janairu, Alhamis da ta gabata a birnin Asaba, nan Jihar Delta.

Ko da shike mun sanar a Naija News makonnai da suka wuce da cewa Hukumar (INEC) ta gargadi ‘yan jam’iyyar PDP da cewa su yi shiru da ƙoƙarin koyawa hukumar INEC yada zata tafiyar da ayukan ta.

Hukumar INEC sun fadi wannan ne a lokacin da suke mayar da martani ga zargin da Jam’iyyar PDP ke yi wa Hukumar akan sanya Amina Zakari matsayin mai kulawa da karban rahotannan zabe. wannan matakin ne Jam’iyyar PDP suka ce basu amince da ita ba da zargin cewa Amina Zakari dangi ce ga shugaba Muhammadu Buhari.

Advertisement
close button