Connect with us

Labaran Najeriya

An bada naira Miliyan 45 ga yankuna don ‘sayen hankalin mutane ga fitar ralin Buhari – inji PDP

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kakakin yada yawun hidimar zabe na Jam’iyyar PDP, Buba Galadima, ya ce Gwamnatin Tarayya ta ba da tallafin kudi ga kananan hukumomi a kasar don jama’a su fito ga yawon ralin Buhari.

“Kimanin Naira miliyan N20m zuwa naira miliyan N45m aka bayar ga hukukomin kasa don sayen hankali mutane ga fitar yawon rali na Shugaba Muhammadu Buhari” inji Buba.

Muna da sani a Naija News da cewa Galadima ya gabatar da wannan zargin ne a ranar Lahadi da ta gabata a lokacin da yake wata tattaunawa ga batun siyasa a wata gidan talabijin.

“A kowace hidimar yawon neman zabe da Muhammadu Buhari ya je a Jihohin da Jam’iyyar APC ke shugabanci, Jam’iyyar na biyan kananan hukumomin Jihohin kudi daga Naira Miliyan 20m zuwa Miliyan 45m don sayan hankali da lokacin jama’ar ga fitar yawon rali. Daga Buhari ya fara gabatarwa, sai kawai ka gan cewa jama’a sun fara janye wa daga taron, don daman sun zo ne don su cika arjejeniyarsu na fitar rali da aka biya su” inji Buba.

Mallam Buba Galadima ya kara da cewa Jama’a sun fito makil a Jihar Kaduna harma da Jihar Kano a lokacin da Alhaji Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP ya ziyarci Jihohin, fiye da yadda jama’a suka marabci Buhari.

“Fitar yawon neman zabe da Kwankwaso ma ya gudanar a karamar hukuma daya ta fi yawar jama’a bisa yawon rali da Buhari ya yi” inji Galadima.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Babban rikici ya barke tsakankanin ‘yan shirin fim na Kannywood akan kudin da Sanata Bukola Saraki ya raba wa magoya bayan Jam’iyyar PDP a Kannywood.

Mun samu sani da cewa Ummi Ibrahim (ZeeZee) da Zaharaddeen Sani sun yi barazanar kai karar junan su akan kudin da aka bawa kungiyar don kadamar da yakin neman zabe.

“Abin mamaki ne ganin cewa wanda ke barazanar yaki da cin hanci da rashawa ya daga hannun shahararan mai Makirci da marasa gaskiya da cewa shi ne dan takaran su” inji Galadima.

“Mun ga irin wannan a Jihar Kano, inda shugaba Muhammadu Buhari ya daga hannun gurbataccen mutum da duka duniya suka sani da halin cin hanci da rashawa, har Buhari ya daga hannun sa da cewa nasu ne wannan” .

“Marabtan mutane daga kasar Nijar ya bayyana da cewa zasu kawo mutane daga kasar don jefa masu kuri’a” inji shi.

Kalli bidiyon, inda Buba Galadima ya yi wannan bayanin;