Connect with us

Labaran Najeriya

APC: Ina Murna mara matuka da Yemi Osibanjo – inji Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana murnan sa da irin abokin takara da ya ke da shi, watau hadewar sa da Farfesa Yemi Osibanjo.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo ya yi wata hadarin jirgin sama a ranar 2 ga Watan Fabrairu, 2019 a lokacin da yake hanyar zuwa Jihar Kogi ranar Asabar da ta wuce don gudanar da yakin neman zabe a Jihar.

An bayyana a rahoto da cewa jirgin ta kihe ne da Farfessa Yemi da mabiya bayansa a yankin Kaba, Jihar Kogi. ko da shike ba abin da ya faru da ko daya daga cikin wadanda ke cikin jirgin.

Bayan hadarin ma, Farfesa Yemi ya cigaba ne da hidimar sa a Jihar.

Ganin irin wannan mazantaka na Yemi Osibanjo, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jinjina da kuma yaba wa Osibanjo da irin kuzari da yake da ita da kuma mazantakarsa.

“Na Gode wa Allah da kare mataimaki na, Farfesa Yemi Osibanjo daga hadarin jirgin sama da ya yi a ranar Asabar da ta gabata” in ji Buhari.

“Ina yaba wa mataimaki na da kuzari, kokari da kuma irin karfin lamirin zuciya da ya ke da shi, harma da iya ci gaba da hidimar yakin neman zaben bayan hadarin da ya faru da shi a ranar” wannan shi ne bayyanin Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, 3 ga Watan Fabrairun da ta gabata, kamar yadda aka bayar daga bakin Kakin yada yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a birnin Abuja.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa a baya Farfesa Yemi Osibanjo ya gabatar a wata bayani da cewa, so ta gaske shugaba Muhammadu Buhari ke da shi ga kasar Najeriya.

Shugaba Buhari ya bayyana da cewa ya na murna kwarai da gaske da samun mataimaki irin Farfesa Yemi Osibanjo.

Ya yi addu’a da cewa Allah ya bawa Osibanjo da wadanda abin ya faru da su karin karfi, lafiyar jiki da kuma kuzari na shugabancin kasar nan.

“Ina bugun gaba da kuma jinjina maka da irin sadaukarwa da kake akan kasar Najeriya” inji Buhari.

Hadarin jirgin da ya faru Asabar da ta wuce ya kumshi mataimakin shugaban kasa ne, Farfesa Yemi Osibanjo da wasu maabiya tara 9 a hanyar zuwa Kabba, a Jihar Kogi.