Uncategorized
Jaru na jiran wanda ya karbi cin hanci, Hukumar INEC ta gayawa mallaman zabe

Hukumar gudanar da zaben kasa, INEC ta umurci mallam zabe da guje wa karban cin hanci da rashawa wajen gudanar da aikin zaben tarayya da ke gabato wa.
Mista Festus Okoye, shugaban fasaha ga lamarin zaben kasa ya gabatar da wannan umurnin a bayanin sa da manema labarai a birnin Abuja.
Ya ce, “zamu gabatar da sakamakon zaben ne ta hanyar da doka ta bayar a zaben shekaran nan”
“Duk wanda ya samu tabbaci ko wata shaida na zargin da ake wa Hukumar INEC da cewa ta bayar da katunan zabe ga mallaman addinai a yankun, ya kawo irin wannan shaidar, ba zamu jefar da irin wannan shaidar ba” in ji shi.
Muna da sani a Naija News Hausa da cewa ana zargin Hukumar INEC da shirin yin makirci ga zaben 2019, har da cewa hukumar ta bayar da katunan zabe ga mallaman addinai don raba wa jama’ar su idan zabe ta gabato.
“Wannan zargin ba gaskiya bane, amma idan akwai wanda ya ke da shaida da tabbacin wannan, ya yi kokarin kawo shaidar sa ga hukumar” inji Mista Festus.
“Muna a shirye don kadamar da zabe mafi cancanta a kasar Najeriya kuma muna shirye don daukar mataki ta musanman kan duk mallamin zabe da ya karbi cin hanci da rashawa wajen gudanar da zabe daga hannun duk wani dan siyasa ko rukuni” in ji shi.
Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana murnan sa da gaske da shirin da Hukumar INEC ke yi game da zaben 2019.
Festus ya karshe bayanin sa da cewa, Hukumar za ta biya kowani mallamin zabe da ya karbi cin hanci daga ‘yan siyasa kudin aikin sa, amma bayan haka zasu dauki mataki akan halin da ya aikata na karya doka da mutuncin Hukumar.
Karanta wannan kuma: #BabaYaKasa: Ba mu son ka kuma, ‘yan Najeriya sun gayawa Buhari