Kiki Osibanjo ta mayar da Martani ga hadarin babban, Farfesa Yemi Osibanjo

Diyar mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kiki Osinbajo ta nuna halin diya macce mai kirki da kuma hankali da irin martani da ta mayar ga wasu da ke fade-faden su game da tsohon ta bayan hadarin da yayi a ranar Asabar da ta gabata.

Wasu, sun aika a yanar gizo da cewa basu ji dadi ba da Farfesa Yemi Osibanjo bai mutu ba a hadarin.

Da diyar ta ga hakan, maimakon ta mayar masu da zafi, sai ta mayar masu kalma mai sanyi da kuma addu’a.

Wannan ya bayyana ko ita wace irin macce ce.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo ya yi hadarin jirgin sama tare da wasu mabiya bayan sa a yayin da suke kan hanyar shiga Kabba, Jihar Kogi.

Hadarin ya faru ne a safiyar ranar Asabar da ta gabata, 2 ga watan Fabrairu 2019, kamar yadda muka sanar a Naija News da baya.

Ga bayanin Kiki Osibanjo da masu bukatar tsohon na ta da mutuwa kamar haka a shafin nishadarwa ta twitter.