Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litinin, 4 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litinin, 4 ga Watan Fabrairun, 2019

 

1. Atiku ya yi kuka da hawaye game da irin amincewa da ya samu

Dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce hawaye sun fado masa saboda irin amincewa da goyon baya da ya ke samu a gabatowar zaben tarayya da ke gaba a kasar Najeriya.

Mun samu tabbacin wannan ne a Naija News ta sakon da tsohon Mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya aikowa gidan labaran mu a ranar Lahadi da ta gabata.

2. Tinubu ya mayar da martani akan shirin makirci da ake game da Gwamna Ambode

Babban shugaban Jam’iyyar APC na tarayya, Bola Tinubu ya bayyana shirin makircin tsige Gwamnan jihar Lagos, Akinwunmi Ambode a matsayin “rikice-rikice tsakanin ‘yan majalisa da Shugabannai” a jihar.

Naija News ta samu tabbacin cewa shugabannin Jam’iyyar APC a Jihar Legas sun yi zaman tattaunawa tsakanin Gwamnoni da ‘yan Majalisu don magance tsatsaguwa da rikicin da ke tsakanin rukuni biyun na shirin tsige Gwamnan Jihar.

An yi gudanar da zaman tattaunawar ne a Marina, a nan JiharLegas.

3. Biafra: Dalilin da ya sa na gudu daga Najeriya kamar Mandela – Nnamdi Kanu

Shugaban kungiyar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ya ce, “Na gudu ne daga kasar Najeriya kamar Nelson Mandela saboda Shugaba Muhammadu Buhari ya turo rundunar sojojin Najeriya zuwa gidana don su kashe ni”.

Muna da tabbacin wannan bayyanin a Naija News da cewa Nnamdi Kanu ya gabatar da bayyanin a wata sanarwa da ya bayar a gidan Radiyon Biafra da ke a birnin London ta United Kingdom a ranar Asabar da ta gabata.

4. Ba Jirgin mu ne ya fadar da Farfesa Yemi Osinbajo ba – inji Sojojin Sama (NAF)

Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya sun mayar da martani game da zargin da ke yawo na cewar jirgin sama da ya fadi da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo na su ne.

Sojojin sun yi musun cewa Jirgin samar da sunan Augusta AW139 da ya fadi da Osibanjo a ranar Asabar da ta gabata a yayin da shugaban ke kan tafiya zuwa Jihar Kogi don gudanar da yakin neman zabe, cewa ba ta su ba ce, kuma basu da wata liki da wannan jirgin, in ji su.

5. Gwamnatin tarayya ta biya naira miliyan 45 ga yankuna don ‘sayen hankalin mutane ga fitar ralin Buhari – Buba Galadima

Kakakin yada yawun Jam’iyyar PDP, Buba Galadima, ya ce Gwamnatin Tarayya ta ba da tallafin kudi ga kananan hukumomi a kasar kimanin Naira miliyan N20m zuwa naira miliyan N45m don sayen jama’a ga fitar yawon rali na Shugaba Muhammadu Buhari.

Muna da sani a Naija News da cewa Galadima ya gabatar da wannan zargin ne a ranar Lahadi da ta wuce a lokacin da yake gabatarwa a wata shirin tattaunawar siyasa a gidan talabijin.

6. PDP: Nnamdi Kanu ya ce, Alhaji Atiku Abubakar dan Kamarun ne

Shugaban kungiyar ‘yan Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ya ce dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar dan Kamarun ne ba dan Najeriya ba.

Nnamdi Kannu ya yi wannan zargin ne a ranar Asabar da ta gabata a gidan Radiyon Biafra da ke birnin London, a  United Kingdom.

7. Kada ku yi fitar yakin neman zabe a Jihar Rivers, Gwamna Wike ya gargadi Jam’iyyar APC

Gwamna Nyesom Wike, Gwamnan Jihar Rivers ya gargadi jam’iyyar APC da cewa kada su yi fitar yakin neman zabe a Jihar ganin cewa zaben tarayya ta gabato.

Gwamnan ya zargi Jam’iyyar APC a Jihar da cewa suna kadamar da yakin neman zabe ne kawai don tayar da hankali da kuma shirin makirci ga sakamon zabe tarayya a Jihar.

8. Rundunar Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram 4

A ranar Asabar da ta gabata, Rundunar Sojojin Najeriya sun hau ‘yan Boko Haram da hari har sun kashe mutum hudu daga cikin su.

Ganawan wutar ya faru ne tsakanin Rundunar Sojojin Najeriya da ‘yan Boko Haram a nan kauyen Malumfatori da ke yankin Abadam, a Jihar Borno inda rundunar sojoji suka lashe ‘yan ta’addan da nasara ta kashe mutane hudu da kuma ribato wasu makaman yaki daga ‘yan ta’addan.

Ka samu karin labaran Najeriya daga shafin Naija News Hausa

Advertisement
close button