Connect with us

Uncategorized

Toyin Abraham ta yi bayani game da soyayyarta da Yemi Osibanjo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wata shaharrariyar ‘yar shirin fim na Najeriya, mai suna Toyin Abraham ta mayar da martani game da zargin da ake mata na cewar tana da halakar soyayya da mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osibanjo.

A bayanin ta, Toyin ta ce, “Kudi ba matsala ta bane idan ana maganar soyayya”.

Wannan shi ne bayanin ta kamar yadda ta aika ga daya daga cikin masoyanta a shafin shirin fim dake zargin ta da soyayya da Farfesa Osibanjo.

Muna da labari a Naija News da cewa Toyin Abraham ta aika wa Farfesa Yemi Osibanjo sakon tayi da murna akan irin hadarin jirgin sama da yayi, da kuma tsira daga hadarin ba da wata rauni ba.

Ganin irin wannan sakon, masoyan ta a shafin shirin fim na Nollywood suka fara zargin ta da cewa tana da halakan soyayya da Osibanjo.

“Ni ba ragguwa ba ce, kuma ni macce ce mai kuzarin aiki”

“Ku yi bincike na ga jama’a, ni bana fadawa ga tarkon soyayya wai don kudi, ina soyayya ta ce don Son da ke a zuciya ta” in ji ta

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Jaruma, Jamila Umar Nagudu, ta fada a baya da cewa “Ba na son Auren mai kudi ko kadan, kuma kazalika ba na son auren talaka

Shaharariyar ‘yar wasan fim na Kannywood din ta bayyana wannan ne a wata zaman ganawa da ta yi da gidan telebijin na ‘Kannyflix Programme’ a wajen shirin su na ‘Mujallar Tauraruwa’.