Connect with us

Uncategorized

Harin Boko Haram a Jihar Adamawa ranar Litini da ta gabata

Published

on

at

advertisement

‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai wata sabuwar hari a karamar hukumar Madagali ta Jihar Adamawa a daren ranar Litinin da ta gabata.

Sun fada wa kauyuka Ukku a yankin, Kauyen Shuwa, Kirshingari da kuma kauyen Shuari. Rahoto ta bayar da cewa mutane ukku suka mutu sakamakon wannan harin, sun kone shaguna 20 da wuta, motoci ukku da kayaki masu tsadar gaske suka wuce da su duka.

“Sun fado wa kauyukan ne da hari a daren Litinin, sun samu kashe mutane ukku, suka kuwa kone shaguna 20, sa’annan suka tafi da kayaki masu tsadar gaske da motoci ukku” inji wani dan tsaro da ke a yankin da abin ya faru.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa a baya, ‘Yan hari da bindiga sun sace Hamisu Mijinyawa, Ciyaman na Jam’iyyar APC a yankin Demsa, Jihar Adamawa.

Mazaunan yankin su bayar da cewa ‘yan ta’addan sun shiga kauyan da motoci misalin karfe 7pm na daren ranar Litinin. Sun fada wa Madagali da hari har sai da Rundunar Sojojin Najeriya dake a Gulak da Michika suka iso wajen don ganawar wuta da ‘yan ta’addan.

“Ganawar wuta tsakanin ‘Yan ta’addan da Sojojin Najeriya ya dauki tsawon awowi biyu kamin ‘yan ta’addan suka gudu bayan sun samu kashe mutane ukku” inji mazaunan kauyan.

Muna da sani a Naija News da cewa Hukumar INEC ta ambaci yankuna ukku da za a gudanar da zabe a karamar hukumar Madagali, abin tsoro shine, Kauyen Shuwa na daya daga cikin mazaba da hukumar INEC ta sanar da ita.

Rundunar sojojin, Bataliyan Mubi ta jagorancin Lt. Col Haruna da hadin gwuiwan Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar sun dauki mataki akan wannan hari.

“Hadin kan Hukumomin tsaro kasa biyun ya magance wannan hari kuma zata ci gaba da samar da tsaro a yankin” inji Mai yada labaran tsaro na Jihar Adamawa, DSP Othman Abubakar.

Karanta wannan kuma: Rundunar Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram 4 a Jihar Borno