Connect with us

Uncategorized

Kasar Nijar, Chad, Mali da Kamarun, Ku Janye wa lamarin Zaben kasar mu Najeriya – Inji Ohanaeze

 

Hadaddiyar Kungiyar Iyamirai da aka fi sani da ‘Ohanaeze Ndigbo’ sun bada umurni da cewa ba wata rukuni ko kasar waje da zata jefa kuri’a ga zaben Najeriya da ya gabato.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa mutane da dama daga kasar Nijar sun halarci hidiman rallin da shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC suka yi a Jihar Kano a ‘yan kwanaki da ya gabata.

Wadda ganin hakan Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kula da wannan, kuma ya daga yatsa da murya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya shigo da ‘yan ta’addan kasar Nijar wajen hidimar yakin neman zaben sa a Jihar Kano.

Chucks Ibegbu, Sakataren Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ya gabatar da ra’ayin Kungiyar a ranar Litinin, ga Watan Fabrairun, 2019 da cewa ba za su yadda wasu daga wata kasa ba su shiga lamarin zaben kasar.

“Ba zamu yadda ba, Kasashe kamar Nijar, Chad, Kamarun, Mali da wasu kasashen Afrika ba za su sanya hannu ba ga lamarin zaben kasar mu” in ji Ohanaeze.

“Saboda hakan mun bukace su da janye hannun su ga lamarin zaben kasar mu”

“Bari Hukumar INEC hade da Hukumomin Tsaron kasa su guje wa wannan damar, ko kuma su kalubalanci kansu idan wata abu ta faru a abaya”.

Kalli bidiyo yadda jama’a suka fito makil ga marabtan Atiku Abubakar, Dan takaran shugaban kasa a Jam’iyyar PDP:

https://www.youtube.com/watch?v=wHAw_T7dKl4

Advertisement
close button