Connect with us

Uncategorized

Ku zabi mijina Atiku Abubakar, Gwanatin sa za ta dakatar da Matsalar Jintsi – Jennifer Abubakar

 

Matan dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Jennifer Abubakar ta bayyana ga mata da cewa su zabi mijinta, Alhaji Atiku Abubakar. “Yin hakan zai magance matsalar daman furci da kuma banbancin jintsi tsakanin namiji da ‘ya na macce wajen gudanar da ayukan kasa” inji Jennifer.

Jennifer ta gabatar ne da wannan ga matan Jihar Cross Rivers a wata ganawar tattaunawa da ta yi da matan Jihar ranar Litinin da ta gabata.

“Ku je ku karbi katunan zaben ku daga Hukumar INEC, Akwai katunan zabe da yawa da ba a karba ba daga hannun hukumar”

“Dole ne mu fara yakin da karban katunan zaben mu, itace karfin mu, kuma dole sai da ita zamu iya bayyana zabin mu” inji ta.

Jennifer ta kara da cewa dakatar da matsalar jintsi na daya daga cikin abubuwan da Gwamnatin PDP za ta kaddamar inda ta shiga mulki.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa matan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari a baya ta yi ganawa da mata don neman goyon bayan su da sake zaben mijinta ga zaben 2019 da ta gabato.

“Ku tabbatar da cewa, Daga ku har jama’ar gidajen ku duka sun jefa wa PDP kuri’ar su ga zaben tarayya ta ranar 16 ga Watan Janairu,2019″ inji Jennifer Abubakar.

“Talauci mugun abu ce, kuma dole ne muyi yaki da shi ta zaben PDP ga mulkin kasar Najeriya”.

A zaman tattaunawar, Matan Gwamnan Jihar Cross River, Dr Linda Ayade, ta bayyana godiyar ta ga Alhaji Atiku Abubakar da ziyarar sa a Jihar Cross Rivers, “wannan ziyarar ya kara karfi da danko zumunci tsakanin matan Jam’iyyar PDP a Jihar mu ” inji Linda.

Ta kara da cewa kashi dari na jama’ar Cross Rivers duk ‘yan jam’iyyar PDP ne, kuma za su jefa kuri’ar su ga Jam’iyyar PDP idan ranar zaben ya iso.

Matan Atiku, Jennifer Abubakar ta hade ne da Matan abokin takaran mijinta, Malama Margaret Obi, watau matan Peter Obi, abokin takaran Alhaji Atiku Abubakar a Jam’iyyar PDP ga tseren shugaban kasa.

Matan biyu su kaddamar da wata shiri na tallafa wa mata a Jihar Cross Rivers.

Karanta wannan kuma: Toyin Abraham ta yi bayani game da soyayyarta da Yemi Osibanjo

Advertisement
close button