Connect with us

Uncategorized

Barista Muhammad Goronyo yayi murabus da PDP ya komawa Jam’iyya APC

 

Kwamishanan Yada Labarai da kuma Ciyaman na Kwamitin Jam’iyyar PDP a Jihar Sokoto, Barista Bello Muhammad Goronyo ya janye daga Jam’iyyar PDP, ya komawa Jam’iyyar APC.

Kamar yadda muka sanar yau a shafin Manyan Labaran Jaridun Najeriya da cewa Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal a ranar Talata da ta gabata, ya dakatar da Kwamishinan Bayanai, Barista Bello Muhammad-Goronyo, wai don ya koma wa Jam’iyyar APC.

Gwamnan ya dakatar da shi daga matsayin sa a Jihar don janye wa daga tsohon Jam’iyyar sa, PDP da komawa Jam’iyyar APC.

Goronyo ya sanar da komawar sa a Jam’iyyar APC ne a lokacin da Jam’iyyar APC ke hidimar ralin su a karamar hukumar Wamakko, a Jihar. Wannan janyewar na sa ya zo daidai ne da lokacin da Jam’iyyar PDP ke na su hidimar rali a hukumar da Gwamna Aminu Tambuwa ke cikin ta.

Dan takaran Gwamnan Jihar Sokoto a Jam’iyyar APC, Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto, ya yaba wa Goronyo da wannan mataki na sa na dawo wa ga Jam’iyyar APC.

Barista Bello Muhammad Goronyo ya fada da cewa “Na dawo ga Jam’iyyar APC, Sanata Aliyu Wamako Uba ne gareni, kuma ina bugun gaba da shi. shugaba ne mai gaskiya” inji Goronyo.

“Ko da shike na yi kuskure a baya, amma na bukaci a yafe mini, kuma zan yi iya kokari na da ganin cewa na goyawa ‘yan takaran Jam’iyyar APC baya a ko ta wani shahe ga zabe na gaba”

Karanta wannan kuma: An bayar da naira Miliyan 45m ga yankuna don sayen hankalin mutane ga fitar ralin Buhari – Mallam Buba Galadima

Ganin matakin da Goronyo ya dauka, Sanata Wamakko ya marabce shi zuwa Jam’iyyar APC, ya kara da kwantata shi a matsayin Da mai biyayya ga manya, “Na ji dadi sosai da wannan” inji Wamako.

Advertisement
close button