Connect with us

Uncategorized

Gidan Kwanan ‘Yan Makaranta Jami’ar Wudil, a Jihar Kano ta Kame da Wuta

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Ma’aikatan Hukumar Kashe Kamuwar Wuta ta Jihar Kano sun gabatar da cewa wuta ya kame Gidan kwanan ‘yan makarantan Jami’ar Fasaha wadda aka fi sani da suna, ‘Kano University University of Science and Technology’, Wudil.

Mun samu tabbacin hakan ne a Naija News daga bakin kakakin yada yawun Hukumar Kashe Kamuwar Wuta na Jihar, Mallam Saidu Mohammed.

“Gidan kwanan ‘yan Jami’ar ya kame da wuta ne sanadiyar karfin wutan lantarke da aka samar masu da ita a wajen” inji Saidu.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa An yi wata hadarin wuta da ya kone shaguna a kasuwar Mariri da ke a Jihar Kano a nan yankin Dawakin.

Mallam Saidu ya bayyana da cewa kimain dakuna 30, Makewayi 20 da dakunan girki 4 suka kone kurmus da wuta.

“Mun karbi wata kirar gaggawa ne daga wani mai suna Alhaji Sagiru da cewa wuta ya kamu a makarantan Jami’ar a misalin karfe 09:52 na daren ranar Talata 5 ga Watan Janairu da ta gabata” inji shi.

“Mun isa wajen ne a misalin karfe 10:21 na dare bayan karban kiran don kashe kashe wutar da kuma hana yaduwarta”

“Ko da shike babu wanda ya mutu a wannan kamun wutar saboda ‘yan makaranta na gida saboda yajin aiki da aka soma watannai da suka shige”.

Karanta kuma: Babban shugaban Sanatocin Najeriya, Sanata Bukola Saraki ya bayyana bakincikin sa game da ‘yar uwar Sanata Kabiru Marafa da aka kashe da kuma mijin da aka sace a Jihar Zamfara.