Connect with us

Labaran Najeriya

Karanta sakon ‘Yan Najeriya zuwa ga shugaba Muhammadu Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci Jihar Ekiti a ranar Talata, 5 ga Watan Janairu da ta gabata don yawon hidimar neman sake zabe.

Muna da tabbaci a Naija News da cewa shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari yayi wata furci a wahen hidimar neman zaben, In ya fada da cewa Gwamnatin sa ta hau wannan mulki ne a shekara ta 2005, maimakon cewa shekara ta 2015.

“Ni, da Jam’iyyar APC mun hau kan mulkin Najeriya ne a shekarar 2005” inji Buhari.

Kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa da safiyar nan a Manyan Labarun Jaridun Najeriya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya fada da cewa, shi da Jam’iyyar sa sun shiga shugabanci kasar Najeriya ne a shekara ta 2005. Ko da shike shugaban na son ne ya ce sun hau mulki ne a ranar 29 ga Watan Mayu, a shekara ta 2015.

Shugaba Muhammadu Buhari yayi wannan kuskuren kalma ne a yayin da yake batun tunawa Jama’a da cewa shi da Jam’iyyar APC ba su manta da alkawalan da suka yi ba a lokacin da suka hau mulki a shekara ta 2015.

A halin yanzun bidiyon wannan hidimar ya mamaye ko ta ina a yanar gizon nishadarwa.

Ga kadan daga bayanin ‘yan Najeriya da suka yi bayan da Buhari ya yi wannan kuskuran furci.

https://twitter.com/lollypking/status/1092858588287172608

https://twitter.com/SocialReflector/status/1092817770746650625