Connect with us

Labaran Najeriya

APC: Ba zan canza daga Adalci na ba – Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Muhammadu Buhari, a ziyarar hidimar neman sake zabe da ya je a yankin Markudi, Jihar Benue ya bayyana ga Jama’ar Jihar da cewa idan har an kara jefa masa kuri’a, kuma ya lashe tseren takaran shugabancin kasar, ba zai canza ba daga adalcin sa.

“Zan ci gaba da halin adalci na da kuma shugabanci ta kwarai kamar yadda na ke yi a yanzu, idan har kun jefa mani kuri’ar ku, kuma ya lashe zaben Watan Fabrairu da ya gabato.

Wannan shi ne bayyani shugaba Muhammadu Buhari a yayin da yake gabatarwa ga jama’ar yankin Makurdi, babban birnin Jihar Benue.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa shugaba Muhammadu Buhari da ‘yan Jam’iyyar APC sun ziyarci Jihar Benue a ranar 6 ga watan Fabrairu, don kadamar da ralin yakin neman zabe a Jihar.

“Ina tabbatar maku da cewa ba zan canza ba, zan ci gaba da aikata halin adalci, da kuma kuzari. kuma duk wanda ya aikata laifi, zamu dauki mataki akan haka” inji Buhari.

Shugaba Buhari, a yayin da yake wannan bayanin a fillin kwallon kafa na Aper Aku da ke a birnin Makurdi, ya ce “Na bada gaskiya da cewa kun gane, kuma kun yadda da ayukan da muke yi, kuna kuma da muradin ganin cewa an ci gaba da wannan.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Manyan shugabanan Jihar Borno da Gwamnan Jihar, Kashim Shettima sun yaba wa shugaba Muhammadu Buhari da irin kokarin da yake yi, musanman kokarin magance ta’addancin Bokok Haram a wata ganawa da suka yi a birnin Abuja makonnai da ta wuce.

Ko da shike, Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ziyarci Jihar Borno a ranar Laraba da ta gabata, kuma Al’ummar Jihar Borno sun fito makil don nuna ma Atiku goyon bayan su ga zaben 2019.