Connect with us

Labaran Najeriya

Dalilin da ya sa Buhari zai fadi ga zabe a Jihohi Hudu – Yan Shi’a

Published

on

at

Kungiyar Zamantakewar Musulunman Kasar Najeriya (IMN) da aka fi sani da suna ‘Yan Shi’a sun gabatar da dalilan da zai sa shugaba Muhammadu Buhari ya fadi ga zaben 2019, musanman a Jihohi hudu, kamar; Jihar Kaduna, Sokoto, Kano da Birnin Tarayya (Abuja).

“Mutanen Jihohin nan sun rigaya sun gaji da shugabanci da Gwamnatin Muhammadu Buhari” inji su.

Sun kara da cewa, matakin jefa shugaban kungiyar IMN, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, na daya daga cikin dalilin da zai sa Buhari ya fadi ga zaben 2019, musanman a Jihohin na da aka ambata.

Mun ruwaito a Naija News da cewa ‘yan Kungiyar Shi’a sun mamaye birnin Abuja a ranara Talata da ta gabata da barazanar cewa suna a shirye ko da zasu mutu ne, sai sun tabbatar da cewa shugaban su, El-Zakzaky ya samu kubuta daga wannan tsari da aka yi masa tun shekarar 2015.

“Ba zamu ja dabaya ba, sai har mun kubutar da shugaban mu da Matan sa” inji ‘Yan Shi’a.

Kalli bidiyon yadda Kungiyar IMN suka yi Zanga-Zanga a birnin Abuja

Karanta wannan kuma: Gidan Kwanan ‘Yan Makaranta Jami’ar Wudil, a Jihar Kano ta Kame da Wuta