Connect with us

Uncategorized

EFCC: Obasanjo ya sace kudi Dala Biliyan $16

 

Tsohon Gwamnar Jihar Abia, Orji Kalu ya zargi Olusegun Obasanjo, Tsohon shugaban kasar Najeriya da sace kudi Dala Biliyan $16.

“Shi ya jawo cin hanci da rashawa ga gwamnatin Najeriya a shekara ta 1999, dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a tseren zaben 2019, Atiku Abubakar mataimakin sa a shekarun baya na matsayin mugun mutum a can lokacin, amma yanzun nan, ya sanya shi a matsayin mai adalci” inji Kalu.

“Babu mutum mai kirki wajen Obasanjo. Yana son kawai ace shi kadai ne mai adalci a kowani lokaci”

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin sa da kasawa ga iya shugabancin kasar.

Obasanjo ya kara da cewa “Ko da shike Atiku ba Almasihu ba ne, amma ya fi Buhari kirki har sau biyu”.

Orji Kalu ya cigaba da cewa, “Na kalubalanci, Ibrahim Magu, shugaban Hukumar EFCC da yin aikin sa yadda ya kamata, ya kuma kame Obasanjo akan wannan halin na sa”

“Ya sace kudin sashen wutan lantarkin Najeriya kimanin Dala Biliyan $16” inji Kalu.

Kalu ya bayyana hakan ne ga manema labarai a yayin da ya ke sauka daga jirgi a filin jirgin saman Murtala Muhammaed da ke a Jihar Legas, a ranar Laraba da ta gabata.

Ya karshe da cewa, “Obasanjo na son ne ace kowane shugaba da ya hau kujerar shugabancin kasar Najeriya, ya zama shi ke jagoran su” inji Kalu.

A baya, mun tuna da cewa Babban shugaban Jam’iyyar APC na Tarayya, Adams Oshiomole ya fadawa Obasanjo da cewa, “Jama’ar Najeriya ba zasu gafarta maka ba da matakin da ka dauka na bayar da birnin Bakasi ga kasar Cameroon don kana nemar farantawa kanka”

“Ko da ba zamu iya yi maka komai ba, tarihi da ‘yan Najeriya ba zasu yafe maka ba da abin da ka yi” inji Oshiomole.

Advertisement
close button