Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 7 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 7 ga Watan Fabrairun, 2019

 

1. Jam’iyyar PDP ta yi barazanar janye daga yarjejeniyar zaman lafiya ga zaben 2019

Jam’iyyar PDP, a ranar Laraba da ta gabata, sun yi barazanar cewa zasu janye daga yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanya hannu a kan gudanar da zaben kasar Najeriya ta shekarar 2019.

Jam’iyyar sun gabatar da wannan ne sanadiyar furcin da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yayi a ranar Laraba na cewa “Duk wata rukunin kasar waje da ke kokarin kafa baki da lamarin zaben kasar Najeriya za su fuskanci mutuwa”.

2. Gwamnatin Najeriya sun mayar da martani game da zancen Nasir El-Rufai

Shugabancin Najeriya sun mayar da martani game da furcin da gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yayi a ranar Laraba da ta gabata a yayin da yake bayani da gidan talabijin labarai na Najeriya (NTA).

Kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa da cewa, Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna ya yi barazanar cewa duk wata rukunin kasar Turai da ta kafa bakin ta ga lamarin zaben kasar Najeriya, “Za su koma gida kamar gawa”

3. Sanata Saraki yayi kira ga Gwamnatin Tarayya don dakatar da yajin aikin Kungiyar ASUU

Shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayyar a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da kawo yajin aikin Kungiyar Mallaman Jami’a (ASUU) a karshe.

Muna da sani a Naija News da cewa Kungiyar ASUU sun soma yajin aiki ne kusan watannai Ukku da ta gabata akan arjejeniyar da kungiyar ta yi da gwamnatin tarayya da ba a cika ba.

4. Matasan Jihar Benue sun fusata da ziyarar Buhari a Jihar Benue

Matasan Jihar Benue sun fada wa Fillin Wasan Kwallon Kafa da ke a Makurdi, inda shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC suka gudanar da hidimar neman zabe. Matasan sun fito ne da yawan su tare da tsintsiya a hannun su wai don share bakin jini da shugaba Muhammadu Buhari ya shigo a Jihar da ita.

Bayan barin shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC a Jihar, Matasan sun fito makil da tsintsiyar su dan share filin da kuma kone tsintsiyar, watau alaman rashin amincewa da shugabancin Jam’iyyar APC.

5. Za a fara tsarafa takardun sufuri na duniya a Nijeriya – inji Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu ga takardan fahimta da arjejeniya a kan samar da fasfot na shiga kasashe a Najeriya.

An sanya hannun ne ga takardan arjejeniyar ta hannun Abdulrahman Dambazau, Ministan Harkokin Waje tare da Kamfanin ‘Iris Smarts Technology Limited’.

6. Jam’iyyar PDP ta bukaci Hukumar INEC da kara ranaku ga karban katin zabe

Jam’iyyar PDP sun zargi hukumar zabe ta kasa (INEC) ba shirin rike katunan zaben al’umma. PDP ta bukaci Hukumar INEC da karan ‘yan kwanaki kadan don mutane su samu karban katunan su.

Jam’iyyar sun gabatar da wannan ne ta bakin Kakakin yada yawun Jam’iyyar, Mista Kola Ologbondiyan.

7. Hukumar EFCC ta kama masu zamba ta shafin yanar-gizo, sun ribato kudi N31m

Hukumar sun kame wasu mutane biyar da ake zargin su da halin sata da zamba a shafin yanar gizo, a Jihar Legas. EFCC ta samu ribato kudi kimanin Miliyan N31m daga hannun su.

Sunayan wadanda hukumar EFCC ta kame da wannan zargin na kamar haka; Paul Duru, Daniel Effiong, David Gold, Moses Gold da Eke Kelechi.

8. Duk Kasar Waje da ta sa baki ga zaben Najeriya za ta fuskanci mutuwa – El-Rufai

Gwamnar Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yayi barazanar cewa duk dan kasar waje da ta kula ko sa baki ga zaben 2019 zata fuskanci mutuwa.

Wannan itace furcin Nasir El-Rufai a bayyanin sa da gidan talabijin na AIT a

Jin wannan bayyani na El-Rufai, ‘Yan Najeriya musanman manyan ‘yan siyasar kasa sun mayar da martani ga wannan.

Ka samu cikakken labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa

Advertisement
close button