Ba zani bawa kowa gurbi na ba - Mahmood Yakubu (INEC) | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labaran Siyasa

Ba zani bawa kowa gurbi na ba – Mahmood Yakubu (INEC)

Published

Shugaban Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC), Mahmood Yakubu ya bayyana da cewa ba zai bawa kowa gurbin sa ba, na matsayin mai sanar da sakamakon zaben kasa ga Al’umma ga zaben 2019.

Yakubu ya bayyana wannan ranar 7 ga watan Fabrairun, Alhamis da ta gabata a birnin Abuja a lokacin da yake ganawa da Bishofs na Ikklisiyar Katolika.

Ya fadi wannan ne don mayar da martani game da jita-jita da fade-faden mutane akan Amina Zakari da hukumar ta sanya a kwanaki a matsayin mai karban zabunan yankuna.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Hukumar INEC ta sanya Amina Zakari a matsayin mai kulawa da karban zabunan Jihohi da yankuna ga zaben tarayya na 2019.

Ko da shike, ‘yan Najeriya, musanman Jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa Amina Zakari ‘yar uwar shugaba Muhammadu Buhari ce, “Sanya ta a matsayin mai karban zabuna shiri ne na makirci ga zaben 2019” inji su.

A zaman da Yakubu ya yi da Bishofs din Katolika a ranar jiya, Ya bayyana da cewa ba zai bayar da gurbin sa ga wani ko wata ba “Ni kadai ne ke da izinin sanar da sakamakon zaben shugaban kasa, ba zani kuwa bada wannan gurbin ga kowa ba” inji shi.

“Ina kuma kira ga ‘yan Najeriya da su sanar mana da duk wata shirin makirci da suka kula da ita a lokacin zaben 2019”

Karanta wannan kuma: Matasan Jihar Benue sun fusata da ziyarar Buhari a Jihar Benue

 
Kuna iya raba Naija News ta hanyar amfani da maɓallin raba mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa newsroom@naijanews.com.