Connect with us

Uncategorized

Kannywood: Dalilin da ya sa na koma Jam’iyyar PDP – Adam A. Zango

 

Shahararen dan shirin Fim na Kannywood, Adam A. Zango ya bayyana dalilin da ya sa ya janye daga Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa kamfanin shirin Fim na Hausa ta rabu biyu akan zaben shugaban kasa ta shekarar 2019. Kamar yadda muka sanar a baya da cewa farmaki ya tashi tsakanin Ummi Ibrahim da Zaharaddeen Sani akan kudin da Jam’iyyar PDP ta bayar ga rukunin Jam’iyyar PDP a cikin Kannywood don gudanar da zaben 2019.

Haka kuma muka sanar da cewa wasu manyan ‘yan shirin fim na Kannywood kamar su Ali Nuhu, Zainab Booth Baba Ari da sauransu sun halarci hidimar ralin yakin neman zaben da shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC suka gudanar a Jihar Kano makon da ta wuce.

A yau Jumma’a, 8 ga watan Fabrairun, ‘yan kwanaki kadan da zaben 2019, Adam A Zango ya hada wata bidiyo inda ya bayyana dalilin da ya sa ya komawa Jam’iyyar PDP.

Mun samu wannan ne a hanyar nishadarwa ta Kannywood a shafin twitter da Youtube.

Kalli bidiyon a kasa; 

Advertisement
close button