Labaran Najeriya
Karanta abinda Maman Osinbajo ta fada game da Shugabancin Buhari
Tsohuwar Farfesa Yemi Osinbajo ta yi bayani game da shugabancin Muhammadu Buhari da danta
A ziyarar da Farfesa Yemi Osinbajo ya kai a gidan su, Maman na sa ta bayyana farin cikin ta da gwamnatin Najeriya a shugabancin shugaba Muhammadu Buhari da yaron ta Yemi Osinbajo.
Tsohuwar mai suna, Olubisi Osinbajo ta fada da cewa “Ya dace a bada dama ga Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari don sake mulkin kasar Najeriya”
“Sun kokarta da gaske, Idan kuwa akwai wanda bai yarda da wannan ba, lallai ba duniyar nan yake ciki ba” inji ta.
“Abin da Buhari da Osinbajo suka yi tsakanin shekaru 3, shugabannan da ba su iya yin hakan ba a shekaru 16 da suka wuce” inji Olubisi.
Wannan shine bayanin Olubisi a lokacin da yaronta, Osinbajo ya ziyarce ta a Somolu, a nan Jihar Legas a yayin da yake zagayen neman zabe na gida da gida.
“Shekaru goma sha shidda 16 da ta wuce, Gwamnatin da bata kadamar da abin da Gwamnatin yanzun nan ta kadamar ba a cikin shekaru 4 kawai” inji ta.
Ta kara da godewa Allah da kare yaronta a hadarin jirgin sama da yayi a Jihar Kogi a ranar Asabar da ta gabata a yayin da Yemi ke yawon yakin neman zabe.
“Na gode kwarai da wannan ziyarar, kuma ina mai godiya ga Allah. Kun san da cewa a ranar Alhamis da ta wuce ina ta rawa da rayeraye ba tare da wata mafari ba? Har na gayawa mutane na da cewa zan yi wa Allah yabo har zuwa maraicen ranar. Ban san da cewa abinda zai faru ke nan a ranar Asabar ba, Na gode ga Allah da wannan” inji ta.
“Yesu Kiristi ne ya bani baiwan yabo, ya kuma ce indinga bashi godiya da yabo, babu wata abin bakin ciki da zai faru da ni. Abin da Allah ya gaya mani ke nan”.
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Diyar mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kiki Osinbajo ta nuna halin diya macce mai kirki da kuma hankali da irin martani da ta mayar ga wasu da ke fade-faden su game da tsohon ta bayan hadarin da yayi a ranar Asabar da ta gabata.
Wasu, sun aika a yanar gizo da cewa basu ji dadi ba da Farfesa Yemi Osibanjo bai mutu ba a hadarin.
Da diyar ta ga hakan, maimakon ta mayar masu da zafi, sai ta mayar masu kalma mai sanyi da kuma addu’a.