Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 8 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 8 ga Watan Fabrairun, 2019

1. An kai ga karshen Yajin Aikin ASUU

A ranar jiya Alhamis, 7 ga watan Fabrairun, 2019, Hukumar Mallaman Jami’o’i da Gwamnatin Tarayya sun kai ga arjejeniya akan dakatar da yajin aikin da Hukumar ASUU ta soma watannai Ukku da ta gabata a kasar.

Hukumar ASUU ta dakatar da yakin aikin ne bayan ganawar awowi biyu da ta yi da gwamnation tarayya a birnin Abuja.

2. Jam’iyyar SDP sun janye daga bayan Donald Duke, sun marawa Buhari baya ga zaben 2019

Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) sun sanar da janye wa daga tseren takaran shugaban kasa ga zaben tarayya da ta gabato.

A gabatar da wannan ne a wata sanarwa da hukumar NEC ta yi a birnin Abuja a ranar Alhamis da ta gabata, da cewa Jam’iyyar SDP sun janye wa tseren takaran, kuma sun mara wa dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari baya ga zabe na gaba.

3. APC ta nemi INEC ta dakatar da zaben takaran gwamnan jihar Rivers

Jam’iyyar APC a Jihar Rivers ta bukaci Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) da dakatar da zaben takaran Gwamnan Jihar Rivers, da cewa gudanar da zaben zai bawa Jam’iyyar PDP daman lashe zaben a banza.

Mun ruwaito a Naija News Hausa, kamar yadda muka sanar a baya da cewa Hukumar INEC ta fada da cewa ba zata raunana ga amincin ta ba.

4. Sani Usman ya sanar da jinkirta daga aikin tsaron kasa

An sanar ga Rundunar sojojin Najeriya da ritayar Brig-Gen Sani Usman, daga mukamin Daraktan Samar da labarai ga Rundunar Sojojin.

Usman ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis da ta gabata a wata sanarwa da cewa ya yi ritaya ne daga rundunar sojojin da kansa.

5. Jama’ar Jihar Katsina sun fito makil don marabtan Atiku Abubakar

A ranar Alhamis 7, ga Watan Fabrairu, 2019, dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci Jihar Katsin don gudanar da hidimar yakin neman zabe.

Jama’ar jihar sun mamaye hidimar ralin don nuna goyon bayan su ga dan takara, duk da cewa shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari mutumin Daura ne a Jihar Katsina.

6. Yarjejeniyar da Nnamdi Kanu, shugaban (IPOB) ya sanya hannu tare da gwamnatin Buhari

Shugaban kungiyar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya rattaba hannu ga yarjejeniyar da Gwamnatin Muhammadu Buhari don kauracewa zaben tarayya a Kudun kasar Najeriya.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa kungiyar ‘yan Biafra a Jagorancin Nnamdi Kanu sun yi barazanar kaurace wa zaben tarayyar kasa a Kudun kasar.

8. Babu wata shirin dakatar da zaben 2019 – INEC

Shugaban Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana da cewa hukumar ba za ta dakatar da zaɓen tarayya da ke gaba ba.

Ya bayyana wannan ne a ranar Alhamis 7, ga Watan Fabrairun da ta gabata a wata jawabi a taron masu ruwa da tsaki.

9. Dalilin da ya sa Buhari zai fadi ga zabe a Jihohi Hudu – Yan Shi’a

Kungiyar Zamantakewar Musulunman Kasar Najeriya (IMN) da aka fi sani da suna ‘Yan Shi’a sun gabatar da dalilan da zai sa shugaba Muhammadu Buhari ya fadi ga zaben 2019, musanman a Jihohi hudu, kamar; Jihar Kaduna, Sokoto, Kano da Birnin Tarayya (Abuja).

“Mutanen Jihohin nan sun rigaya sun gaji da shugabanci da Gwamnatin Muhammadu Buhari” inji su.

Samu cikkaken labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Advertisement
close button